Rungumar noman rani ne zai wadata Najeriya da abinci – Abdulrahman Lawal

Wani fitattacen mai kiwon kaji a jihohin Bauchi da Filato kuma mai gonar kiwon kajin nan ta Yankari Farms, Alhaji Abdulrahman Lawal ya ce mutukar ana son wadata Najeriya da abinci, to dole ne sai an rungumi noman rani a kasar nan. Alhaji Abdulrahman Lawal ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da […]

Rungumar noman rani ne zai wadata Najeriya da abinci – Abdulrahman Lawal

Wani fitattacen mai kiwon kaji a jihohin Bauchi da Filato kuma mai gonar kiwon kajin nan ta Yankari Farms, Alhaji Abdulrahman Lawal ya ce mutukar ana son wadata Najeriya da abinci, to dole ne sai an rungumi noman rani a kasar nan. Alhaji Abdulrahman Lawal ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya a Jos, inda ya ce babu yadda za ay i noman damina kadai da ake yi a Najeriya ya wadata Najeriya da abinci. Haka kuma ya ce gaskiya wannan gwamnati tana da kyakyawar niyya, wajen bunkasa aikin noma a kasar nan. Amma matsalar ita ce idan za a dogara da noma sau daya a shekara, wato noman damina to akwai matsala. Sai an kama noman rani haikan, wannan ne zai taimaka wajen bunkasa aikin noma a Najeriya.

“Duk kasashen da suka ci gaba a duniya kan aikin noma, suna hadawa ne da noman rani. Idan ba a kawo maganar noman rani a Najeriya ba, za a ci gaba da samun matsala musamman kan masara da waken soya da kamfanoni suke sarrafawa. Za mu iya noman rani a Najeriya, kuma idan muka rungumi noman rani kamfanoni da dama za su zo daga waje, su kafa kamfanoninsu a kasar mu,” inji shi. 

Alhaji Abdulrahaman Lawal ya ce masu kiwon kaji a Najeriya suna fama da matsalolin rashin cinikin kwai da tsadar kayayyakin abincin kaji, kamar masara da waken soya da gyada da kayayyakin da ake hada abincin kaji da su.

Ya ce  kullum farashin wadannan kayayyaki tashi yake yi,  a yayin da kullum farashin kwai kuma yake kara sauka kasa, ga kuma rashin cinikin kwan saboda halin matsin da ake fama da shi a kasar nan. Wadannan matsaloli sun kawo cikas ga kiwon kaji a duk fadin kasar nan, don haka yanzu harkokin kiwon kaji ya shiga cikin wani mawuyacin hali a Najeriya.

Ya ce sakamakon wadannan matsaloli yanzu masu gidajen kaji da dama sun rufe gonakinsu, a wurare da dama na kasar nan. Don haka ya zama wajibi gwamnati ta tashi ta ceto harkokin kiwon kaji daga durkushewar da ya tasar wa yi a yanzu haka kasar nan.