Rusa masallaci: Kungiyar Matasan Arewa ta zargi Wike da neman rarraba kai
Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa don Nagartar Kasa, (Coalition of Northern Youth Organisations for National Integrity), ta yi Allah wadai da rusa babban masallacin da ke Unguwar Trans-Amadi a birnin Fatakwal ta Jihar Ribas, da ake zargin Gwamnan Jihar Mista Nyesom Wike da aikatawa. Kungiyar ta bayyana lamarin a matsayin neman burge jama’a ta mummunar hanya […]
Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa don Nagartar Kasa, (Coalition of Northern Youth Organisations for National Integrity), ta yi Allah wadai da rusa babban masallacin da ke Unguwar Trans-Amadi a birnin Fatakwal ta Jihar Ribas, da ake zargin Gwamnan Jihar Mista Nyesom Wike da aikatawa. Kungiyar ta bayyana lamarin a matsayin neman burge jama’a ta mummunar hanya don kawar da hankalin al’umma musamman ’yan jihar a kan al’amuran gwamnati da kuma kara jawo rarrabuwar kai a tsakanin mabiya addinai a kasa baki daya.
A wani jawabi dauke da sa hannun jagoran kungiyar ta kasa, Kwamared Bashir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina, da aka fitar a farkon makon nan, kungiyar ta bukaci shugabannin jama’a daga dukkan bangarorin kasar nan su ja kunnen Gwamnan ta hanyar amfani da matsayinsu da kuma kungiyoyin samar da zaman lafiya da su ke jagoranta.
Haka kungiyar ta yi kira ga al’ummar kasar nan su dauki darasi daga lamarin ta hanyar guje wa zaben jagorori ire-irensa; a matakin shugabanci mai sarkakiya irin na Gwamna da Shugaban Kasa da sauransu.
Kungiyar hadakan matasan Arewan ta ce, bayanan da aka ruwaito Mista Wike na yi cewa Jihar Ribas ta addinin Kirista ce, kfin daukar haramtaccen matakin, ya nuna cewa rusa masallacin bangare ne kawai na shirin kuntata wa al’ummar Musulmi ta hanyar mayar da jihar ta mabiya addinin Kirista kadai, duk da cewa hakan ya saba kundin tsarin mulkin kasar nan da kuma tafarkin adalci, a cewar sanarwar.
A karshe kungiyar ta yaba wa Gwamnan Jihar, Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, kan daukar matakin hanzari da ta ce ya yi ta hanyar cewa zai dauki matakin shari’a don kai karar Gwamna Wike, da dokar kasa ta ba da dama, kamar yadda suka bayyana.