Rusau: Wike ya markaɗe Kasuwar Dare a Abuja
Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike ya rushe Kasuwar Dare da ke yankin Sabuwar Asokoro a Abuja.
Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike ya rushe Kasuwar Dare da ke yankin Sabuwar Asokoro a Abuja.
Ministan yaba da umarnin rushe Kasuwar ne bisa zargin ta da zama matattarar dillalan miyagun ƙwayoyi da ’yan dana da sauran masu aikata laifuka.
- APC da PDP sun saka Wike a kwamitin yakin neman zaben Gwamnan Bayelsa
- DAGA LARABA: Mijina ya sake Ni saboda rashin gaishe shi
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito Darakta Kula da Gine-ginen a Birnin Tarayya, Mr Mukhtar Galadima, na cewa kasuwar ta fara zama barazana ga mazauna yankin da ma masu wucewa.
Mukhtar Galadima ya ce duk da ƙoƙarin da Hukumar Kula da Birnin Tarayya take yi na samar da aminci a birnin, Kasuwar Dare ta zama sansanin masu aikata laifi.
Kasuwar dai tana kan titin Hassan Musa Katsina, kusa da Kpaduma II a Sabon Asokoro.