Rushe gine-ginen da gwamnatin Kano take yi aikin jahilci ne – APC

APC ta ce sayar da filayen gwamnati ba Ganduje ne farau ba

Rushe gine-ginen da gwamnatin Kano take yi aikin jahilci ne – APC

Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta bayyana rushe-rushen da gwamnatin Jihar ke yi a filayen gwamnatin da ta ce an yi ba bisa ka’ida ba, a matsayin ‘aikin jahilci’.

Sai dai jam’iyyar ta roki mutanen da rusau din ya shafa da su yi hakuri su kwantar da hankula sannan su duba yiwuwar tafiya kotu don neman hakkokinsu.

Da yake jawabi a madadin jam’iyyar yayin wani taron manema labarai a Kano ranar Talata, Mataimakin Shugaban jam’iyyar a Jihar, Shehu Maigari, ya ce APC ta yi Allah-wadai da abin da gwamnatin Jihar ta jam’iyyar NNPP ke yi a Jihar.

“Wannan aikin jahilcin na barnatar da dukiyoyin mutane da hanyar neman abincinsu na bukatar muhimmiyar addu’a saboda asarar da mutane suke tafkawa ta biliyoyin Nairori.

“Wannan aika-aikar ta raunata harkokin kasuwanci a fitattun kasuwannin Kantin Kwari da Kofar Wambai, inda aka tsayar da komai cik.

“Matakin na gwamnati ya haifar mutane na lalata dukiyoyin jama’a da rana tsaka da sunan kwasar ganima a irin wadannan wuraren.

“Kazalika, muna kira ga iyaye da su ja kunne ’ya’yansu a kan illar da take tattare da yin amfani da su wajen yin ta’asa. Muna kuma kira ga jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen wado da zaman lafiya a jiharmu kafin a lalata mana jiha.

Da aka tambaye shi mai zai ce kan zargin cewa gwamnatin Ganduje ta lalata taswirar ci gaban jihar ta hanyar raba wa mutane filayen gwamnati, Maigari ya ce ba Gandujen ne ya fara yin haka ba, kuma kowacce gwamnati na yin hakan.

Tun bayan rantsar da Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan Jihar Kano a makon da ya gabata, ya shiga aikin rushe gine-ginen da ya ce gwamnatin da ta gabata ta Ganduje ta yi ba bisa ka’ida ba, saboda abin da ya kira farfado da martabar Jihar.