Rushe kasuwa ya jawo zanga-zanga a Akwanga
Akarshen makon jiya ne ’yan kasuwa sama da 400 wadanda galibinsu mata ne suka gudanar da zanga-zanga kan rushe tsohuwar Babbar Kasuwar Akwanga da Karamar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa da karamar hukumar ta yi. Da take bayyana alhininsu ga wakilinmu a madadin ’yan kasuwar wata mai suna Misis Filicia Ojioma, ta ce mahukuntan karamar […]
Akarshen makon jiya ne ’yan kasuwa sama da 400 wadanda galibinsu mata ne suka gudanar da zanga-zanga kan rushe tsohuwar Babbar Kasuwar Akwanga da Karamar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa da karamar hukumar ta yi.
Da take bayyana alhininsu ga wakilinmu a madadin ’yan kasuwar wata mai suna Misis Filicia Ojioma, ta ce mahukuntan karamar hukumar sun rushe musu dukkan shagunansu da ke kasuwar ba tare da ta sanar da su ba. Ta ce “Mun yi hayar wadannan shaguna kan Naira dubu 200 wadansu har miliyan 4 suka biya na shago guda na tsawon shekara 10.
Kuma wadansu daga cikinmu sun biya kudin shagunan bada dadewa ba aka rushe ba tare da an biya mu diyya ba.”
A cewarta, karamar hukumar ta ba su kwana uku ne kacal kafin ta rushe musu shagunan. Ta ce a halin yanzu babu wani a cikin ’yan kasuwar da aka ba shi shago a sabuwar kasuwar da gwamnatin jihar ta gina a garin Akwanga bayan rushe musu shagunan kamar yadda aka yi musu alkawari.
Misis Filicia ta ce shi ya sa suka gudanar da zanga-zangar don nuna wa gwamnatin jihar da duniya rashin jin dadinsu game da aukuwar wannan lamarin, inda ta ce a halin yanzu wadanda lamarin ya shafa da iyalansu suna cikin mawuyacin hali.
Daga nan sai ta yi kira ga Gwamnan Jihar Injiniya Abdullahi Sule, ya gaggauta sa baki a batun don ba su damar ci gaba da gudanar da kasuwancinsu yadda suka saba.
Da wakilinmu ya tuntubi Shugaban Karamar Hukumar Akwanga Mista Samuel Meshi, ya ce karamar hukumar ta sanar da ’yan kasuwar kuma ta ba su isasshen lokaci, don su koma sabuwar kasuwar kafin a fara rushe-rushen amma suka ki yin haka.
Ya kara da cewa kafin a fara rushe-rushen kasuwar sai da aka gudanar da wani taro na masu ruwa-da-tsaki inda galibin ’yan kasuwar suka amince za su koma sabuwar kasuwar kafin karshen wa’adin da aka ba su.