‘Rushe kasuwarmu ya janyo mana asarar miliyoyin Naira’
Yan kasuwa da ke sayar da kayan abinci a kasuwar abbatuwa da ke unguwar Oko-oba a jihar Legas sun ce matakin da gwamnati ta dauka na rushe kasuwar ya sa sun tafka asara ta miliyoyin kudi.Shugaban masu sayar da tumatir na kasuwar, Alhaji Sama’ila Sa’idu kiru ya ce rushe kasuwar ya sanya su cikin tsaka […]
Yan kasuwa da ke sayar da kayan abinci a kasuwar abbatuwa da ke unguwar Oko-oba a jihar Legas sun ce matakin da gwamnati ta dauka na rushe kasuwar ya sa sun tafka asara ta miliyoyin kudi.
Shugaban masu sayar da tumatir na kasuwar, Alhaji Sama’ila Sa’idu kiru ya ce rushe kasuwar ya sanya su cikin tsaka mai wuya.
Ya ce ‘A yanzu a takaice ba za mu iya kididdige abin da muka yi asara ba, amma mun yi asarar miliyoyin naira sakamakon rusau din da aka yi mana, saboda kasuwa ta tsaya babu wata hada-hada saboda shagaltar da muka yi da abin da ya same mu. Mun yi mamakin yadda gwamnati ta rushe kasuwar rana-tsaka domin lamarin yana kotu kuma kotu ta ba da ummarnin a dakatar da rushe kasuwar, amma gwamnati ta yi kunnen-uwar-shegu ta yi gaban kanta’.
Ya ci gaba da cewa, ‘Tun da magana tana kotu muna sauraren hukuncin da kotu za ta yanke kan lamarin. Saboda haka za mu koma kotu ko da shi lauyanmu ya ce mana mu yi hakuri mu ga abin da kotu za ta zartar.’
Alhaji Sama’ila, wanda ya bayyana cewa za su ci gaba da bin doka da oda kamar yadda suka saba a jihar Legas, ya bukaci ’yan kasuwan da su kwantar da hankulansu.
Shi ma Mista Ola wanda ke sayar da kaji ya bayyana bakin cikinsa dangane da rushe kasuwar da gwamnati ta yi.
Ya ce gwamnati ba ta ba su wa’adi mai yawa ba da za su nemi shaguna a wadansu kasuwannin don ci gaba da kasuwancinsu.
Ya bayyana cewa sashen masu sayar da kaji sun tafka asara mai yawa sakamakon rushe musu rumfuna.
daya daga cikin masu gine-gine a kasuwar Alhaji Sherif Muhammed ya bayyana cewa sun bi duk ka’idar da ta kamata kafin ya yi gini a cikin kasuwar.
To sai dai gwamnatin jihar Lrgas ta dage a kan cewa ta bi duk ka’idojin da suka kamata kafin ta rushe kasuwar.