Masarautar Kano: Abba ya ba da umarnin tsare Sarki Aminu

Ana zaman dardar a Kano a yayin da ake zargin jami’an tsaro daga Abuja suke kokarin shigar da Sarki Aminu Ado Bayero fadar Kofar Kudu sa’o’i kadan bayan an ba wa Sarki Muhammadu Sanusi II takardar aiki.

Masarautar Kano: Abba ya ba da umarnin tsare Sarki Aminu

A yanzu haka ana zaman dardar a Kano a yayin da ake zargin jami’an tsaro suna kokarin shigar da Sarki Aminu Ado Bayero fadar Kofar Kudu sa’o’i kadan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba wa Sarki Muhammadu Sanusi II takardar aiki.

A safiyar Asabar gwamnatin jihar, Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin kama Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da sukan tsare shi.

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu ta ce a matsayinsa gwamnan na shugaban tsaron jihar, ya dauki wannan matakin ne don tabbatar da cikakken tsaro a jihar da kewayenta.

Hakan dai baya rasa nasaba da wasu rahotanni da ke cewar Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero da gwamnati ta sauke yana kan hanyarsa ta komawa fadar Masarautar Kano daga Abuja.

Wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya fitar, ta bukaci magoya bayan Aminu Ado Bayero su fito su tare shi da safiyar Asabar a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano domin raka shi gidan Dabo.

Rahotonni sun bayyana cewa Sarki Aminu Ado Bayero, wanda aka sauke a ranar Alhamis, ya shigo Kano da rakiyar jami’an tsaro wanda ake zargin ya taho da su daga Abuja, suna kokarin shigar da shi cikin fadar da karfin tuwo.

Wannan lamari wanda ba a taba ganin irinsa a Jihar Kano ba ya sa Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf da Mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo da sauran jami’an Gwamnatin suka kwana a fadar ta Kano.

Aminiya ta rawaito cewa an girke jami’an tsaro musamman wadanda ke tare da gwamnan a fadar inda suke jiran ko ta kwana.

Gwamna Abba ya ba da umarnin kamo Sarki Aminu Ado Bayero, kan zargin neman tayar da fitina kwana biyu bayan an tsige shi.

Aranar Alhamis aka sauke shi bayan Majalisar Dokokin Jihar Kano ta rushe sabbin masautun jihar biyar da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro a jihar.

A ranar Juma’a Gwamna Abba ya mika wa Sarki Muhammadu Sanusi II wanda gwamnatin Ganduje ta tube a 2020 ta nada Aminu.

Tun a ranar Alhamis Abba ya sanya hannu kan sabuwar dokar, ya kuma ba wa sarakunan da aka rushe awa 48 su fice daga fada masarautun.

Sauran masarautun su ne na Bichi, Gwarzo, Karaye da kuma Rano.

A jawabinsa Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam, ya bayyana cewa “mun sami labari cewa Dokta Abdullahi Umar Ganduje ne ya je wajen Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, suke kokarin bankara lamarin wajen ganin sun dawo da tsohon Sarkin Kano kujerarsa”

Kwamared Aminu Abdulsalam ya kuma sha alwashin cewa za su ci gaba da zama a fadar har isai sun ga abubuwa sun daidaita.

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi