Rushe Masarautun Kano: APC ta kaura ce wa zaman Majalisa
Ana hasashen sauyin zai kai ga rushe sabbin masarautu da kuma dawo da Sanusi II a matsayin Sarkin Kano
’Yan jam’iyyar APC a Majalisar Dokokin Kano sun kaurace wa zamanta na ranar Alhamis da za ta ci gaba da aikin sauya dokar kada masarautu da nada sarakunan jihar.
A zaman majalisar na ranar Laraba kudirin dokar ya tsallake karatu na daya, inda ake sa ran yin karatu na biyu da na uku a nan gaba.
Al’amuran sun fara kankama a zauren majalisar ba tare fuskar ko mutum daya daga mambobin APC.
Wakilinmu da ke wurin ya ce daga bisani uku daga cikin mambobin APC 12 da ke majalisar sun hallara.
- Sarkin Kano: Sanusi II na shirye-shiryen komawa kujerarsa
- Kotu ta amince wa Dalibai Musulmi sanya Hijabi a Oyo
Aminiya ta ruwaito cewa, jami’an tsaro ɗauke da makamai da suka haɗa da ‘yan sanda da na sibil difens ne suka mamaye wasu muhimman wurare a harabar Majalisar Dokokin a ranar Laraba, yayin da ‘yan majalisar suka fara gyaran dokar majalisar masarautun jihar da ta kafa masarautu biyar.
An soma zaman yi wa dokar kafa masarautun gyara yayin da shugaban masu rinjaye kuma mamba mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Dala, Lawan Hussaini Chediyar ’Yan Gurasa ya gabatar da ƙudirin.
Aminiya ta ruwaito cewa, hatta manema labarai da suka zo cin kasuwar ɗaukar rahoton zaman majalisar na wannan rana sai da aka riƙa tantance su gabanin samun izinin shiga harabar majalisar sa jami’an tsaro suka yi wa dandazo.
Sai dai shugaban marasa rinjaye na majalisar, Abdul Labaran Madari, ya shaida wa BBC cewa ’yan jam’iyyar APC 12 a majalisar ba sa adawa da gyaran matuƙar ba za a rusa ko ɗaya daga cikin masarautun biyar ba.
Haka kuma, Madari ya ce ba za su yi adawa da yi wa dokar gyaran fuska ba matuƙar ba za a tsige Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ba kuma ba za a maye gurbinsa da Sarki Muhammad Sanusi ba.