Rushe Masarautun Kano: Ba a kyauta mana ba —Kabiru Rurum

NNPP ta mayar da martani ga mambanta a Majalisar Wakilai, Kabiru Alhassan Rurum, wanda ya soki Gwamnatin Kano kan rage darajar Masarautar Rano.

Rushe Masarautun Kano: Ba a kyauta mana ba —Kabiru Rurum

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, sanye da jar hula tare da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, a taron bikin dashen itatuwa na shekarar 2024 a Birnin Kwankwasiyya. (Hoto: X/@Kyusufabba)

Jam’iyyar NNPP ta mayar da martani ga mambanta a Majalisar Wakilai, Kabiru Alhassan Rurum, wanda ya caccaki Gwamnatin Kano kan rage darajar Masarautar Rano.

Kabiru Alhassan Rurum, wanda tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano ne, ya nuna rashin jin dadinsa ne a lokacin kaddamar da Makarantar Sakandare ta Kwana ta ’yan mata ta Sojojin Sama a Rano ranar Lahadi.

Rurum wanda shi ke mai wakiltar mazabar Rano, Kibiya, da Bunkure, kuma Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Sojojin Sama, shi ke rike da sarautar Turakin Rano.

Dan majalisar wanda aka zabe shi a karkashin jam’iyyar NNPP bayan ya sauya sheka daga Jam’iyyar APC a shekarar 2023, ya jaddada muhimmancin tarihi da al’adar Masarautar Rano.

“Ina so in tabbatar wa duk wani dan Kano ta Kudu cewa ina matukar adawa da ruguza masarautunmu.

“In tare da masarautar Rano mai daraja ta daya 100 bisa 100, kuma babu wanda zai iya  mayar da mu zuwa matsayi na biyu. Wannan matsayi ne da Allah Ya ba mu.

“Mu zuriyar Autan Bawo ne, muna da dimbin tarihi a kasar Hausa. Mun fahimci kima da darajar da Allah Ya ba mu a matsayinmu na mutanen Rano,” in ji dan majalisar.

An rage darajar masarautar ce bayan sabuwar Dokar Masarautu da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi a baya-bayan nan, inda ta rusa dukkanin masarautun biyar da tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kafa a hukumance.

Dokar ta kuma kafa sabbin masarautu masu daraja ta biyu a Rano, Gaya, da Karaye, kowannensu, inda kowaccensu ke da kananan hukumomi a biyu zuwa uku.

Kafin rushewar, Masarautar Rano ta kunshi kananan hukumomi 10 da suak hada da  Rano, Kibiya, Bunkure, Kura, Tudun Wada, Doguwa, Sumaila, Takai, Garun Malam, da Bebeji.

Amma a karkashin sabuwar dokar, ikon masarautun masu daraja ta biyu zai takaita ne kawai ga kananan hukumominsu, kuma sarakunansu suna karkashin Sarkin Kano.

Da yake mayar da martani kan matsayar Rurum, Shugaban NNPP a Jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya ce jam’iyyar na mutunta ra’ayin dan majalisar.

“A tsarin dimokuradiyya, kowa na da hakkin bayyana ra’ayinsa.

“Muna goyon bayansa saboda matsayar da ya dauke ke nan, kuma ba za mu iya canja masa ba.

“Wannan ba abin da ya shafi harkokin jam’iyya na ne, ra’ayinsa ya fadi kuma yana da ’yanci yin hakan,” in ji Dungurawa.