Rushe ofishin jakadanci: Ghana ta nemi afuwar Najeriya
Shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya nemi afuwar Shugaba Muhamamdu Buhari bisa rushe ginin ofishin jakadancin Najeriya a kasarsa, ya kuma bayar da umarnin bincike a kan lamarin. Shugaba Akufo-Addo ya gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta wayar tarho inda ya nemi afuwa kan rushe ginin ofishin jakadacin Najeriya da ke Birnin Accra a […]
Shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya nemi afuwar Shugaba Muhamamdu Buhari bisa rushe ginin ofishin jakadancin Najeriya a kasarsa, ya kuma bayar da umarnin bincike a kan lamarin.
Shugaba Akufo-Addo ya gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta wayar tarho inda ya nemi afuwa kan rushe ginin ofishin jakadacin Najeriya da ke Birnin Accra a Ghana.
Sanarwar hakan da Mai Taimaka wa Shugaba Buhari ta fuskar Yada Labarai, Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce shugaban na Ghana ya shaida wa Shugaba Buhari cewa ya ba da umarnin binciken lamarin.
A ranar Lahadi ne aka samu rahoto cewa wasu matasa dauke da bindigogi sun rako wata motar rusa gini tare da yin kutse a ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin Accra, inda suka yi barazanar hallaka ma’aikata sannan suka rushe sabon ginin masauki da ake yi a harabar ofishin.
- ‘Yan bindiga sun rusa ofishin jakadancin Najeriya a Ghana
- PDP ta caccaki Buhari kan hari a ofishin Najeriya da ke Ghana
Hakan ya biyo bayan takaddama kan filin wanda wani babban attajiri dan kasar ta Ghana ya yi ikirarin cewa ginin ya shiga cikin filinsa kafin daga baya a sasanta maganar.
“Tun da fari dai a ranar Laraba an kama wasu da ake zargi da rusa ginin, za kuma a gurfanar da su a kotu”, inji Garba Shehu.
Rushe ginin diflomasiyyar Najeriya a Ghana da wasu mutane dauke da bindogogi suka yi ya janyo kace na ce inda wasu ke ganin mahukunta a kasar Ghana na yin ko-ina-kula wajen kare ‘yan Najeriya da ke zaune a kasar tare da dukiyoyinsu.