Rushe shugabannin kananan hukumomi ya jawo cece-ku-ce a tsakanin PDP da APC
Wani dan Jam’iyyar APC a Jihar Katsina Alhaji Alah Muhammed y a ce, rashin adalci ne Jam’iyyar PDP a jihar ta zargi ’yan sanda da hada baki da gwamnati don musguna wa rusassun shugabannin kananan hukumomi 34 da suke ’ya’yan PDP ne da gwamnatin Masari ta rushe a watan Yulin da ya gabata. Alhaji Alah […]
Wani dan Jam’iyyar APC a Jihar Katsina Alhaji Alah Muhammed y a ce, rashin adalci ne Jam’iyyar PDP a jihar ta zargi ’yan sanda da hada baki da gwamnati don musguna wa rusassun shugabannin kananan hukumomi 34 da suke ’ya’yan PDP ne da gwamnatin Masari ta rushe a watan Yulin da ya gabata.
Alhaji Alah Muhammed ya ce, kada PDP ta manta cewa, a lokacin da take mulki a jihar babu irin gudunmawar da ’yan sanda ba su ba ta ba don ganin cewa an kare mutunci da martaba da shugabanninta saboda su ne ke da madafun iko a lokacin. “In har za a iya kare su a lokacin da suke mulki haka za a yi wa duk jam’iyyar da ke mulki a kan abin da ya shafi tsare doka da oda,” inji shi.
Alhaji Alah ya tunatar da PDP cewa, kada ta manta da abin da ya faru a jihar a lokacin da take mulki, inda ya ce ba ma Kwamishina ba, wasu daban sun rika musguna wa jama’a.
Ya tunatar da su abin da su Koko da Bauranya suka yi da kuma abin da ya faru a Majalisar Wakillai inda gwamnatin PDP ta yi amfani da ’yan sanda don hana Shugaban Majalisar shiga ofishinsa a wancan lokacin.
Gwamnati ta yi amfani da dokar da PDP ta kafa a jihar ne, su kuma jami’an tsaro suna tabbatar da ana kiyaye doka da oda ne, amma take zarginsu da hada baki da gwamnati. “Ni ina ganin kamata ya yi PDP ta yi godiya ba zargi ba, saboda an kiyaye mata ’ya’yanta da ita kanta daga fadawa cikin wani yamutsi.
Jam’iyyar PDP ta Jihar Katsina ta zargi Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Usman Aliyu Abdullahi cewa, ya ki mutunta umarnin da wata Babbar Kotu ta bayar a ranar 13/7/2015 na hana gwamnatin jihar rushe shugabannin kananan hukumomin jihar, bayan da gwamnatin a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta bayar da sanarwar rushe shugabannin a ranar Juma’a 10/7/2015, bayan samun amincewar Majalisar Dokokin Jihar.
Kakakin Jam’iyyar PDP na Jihar, Salisu Ali Sukuntuni ya fadi a wata takardar da ya sanya wa hannu a madadin shugabanta kuma aka raba wa manema labarai a ranar Juma’ar da ta gabata jam’iyyar ta zargi Kwamishinan da janye ’yan sanda da masu kare lafiyar shugabannin kananan hukumomin da hana shugabannin shiga ofisoshinsu da gayyatar wasu shugabannin zuwa ofishinsa don yi masu tambayoyi, inda ta yi kira ga Kwamishinan ya bi umarnin kotu har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan shari’ar da ke gabanta.
A martanin da Kwamishinan ’Yan sandan Usman Aliyu Abdullahi da Kakakin Rundunar ya DSP Aminu Abubakar Sadik ya mayar ya ce, shugabannin suna amfana da jami’an tsaro ne a lokacin da suke bisa madafun iko, kuma tunda gwamnati ta rushe su sai aka janye su har sai an ga hukuncin da kotu ta yanke. Ya ce sun tura jami’ansu hedkwatocin kananan hukumomi ne saboda tabbatar da kiyaye doka da oda da kare lafiyar jama’a da dukiyoyinsu da kuma hana barnata kayan gwamnati.