Rushewar gini ya kashe yaro a Osun
Wani gidan laka da ya rushe a karshen mako a harabar Kegbe, da ke hanyar Kajola a Osogbo babban birnin jihar Osun. Ya yi sanadiyyar kashe wani yaro mai suna Jide dan shekara 11. Ginin ya ruftawa yaron ne lokacin da yake wucewa ta kusa da gidan. An dai yi gaggawa kai Jide asibitin unguwar […]
Wani gidan laka da ya rushe a karshen mako a harabar Kegbe, da ke hanyar Kajola a Osogbo babban birnin jihar Osun. Ya yi sanadiyyar kashe wani yaro mai suna Jide dan shekara 11.
Ginin ya ruftawa yaron ne lokacin da yake wucewa ta kusa da gidan. An dai yi gaggawa kai Jide asibitin unguwar Oke-Baale inda likitocin suka ce, a mika shi zuwa wani asibitin.
A hanyar kai yaron asibitin koyarwa na Jami’ar Ladoke Akintola ya rasu.