Ruwa ya ci jami’in kiwon lafiya a Sakkwato

Wani jami’in kiwon lafiya mai suna kasimu Tukur da gwamnatin Jihar Sakkwato ta tura don bai wa yara maganin zazzabin maleriya ya gamu da ajalinsa a ranar Talata da ta gabata a hanyarsu ta zuwa kauyen Bafarawa da ke karamar Hukumar Isa da ke jihar.Babban Jami’in Kiwon Lafiya na karamar Hukuma Isa, Alhaji Ibrahim Tukur […]

Ruwa ya ci jami’in kiwon lafiya a Sakkwato
Ruwa ya ci jami’in kiwon lafiya a Sakkwato

Wani jami’in kiwon lafiya mai suna kasimu Tukur da gwamnatin Jihar Sakkwato ta tura don bai wa yara maganin zazzabin maleriya ya gamu da ajalinsa a ranar Talata da ta gabata a hanyarsu ta zuwa kauyen Bafarawa da ke karamar Hukumar Isa da ke jihar.
Babban Jami’in Kiwon Lafiya na karamar Hukuma Isa, Alhaji Ibrahim Tukur wanda ke cikin ayarin, ya shaida wa Aminiya cewa: “Mun bar Isa zuwa Bafarawa sai muka shiga kwale-kwale saboda gadar da ta hada kauyukan ta karye shekara biyar da suka gabata. Muna tafiya a cikin ruwan sai jirgin ya huje ruwa ya rika shiga cikinsa, inda marigayin ya fara cewa a san abin da za a yi domin shi bai iya ruwa ba. Sai aka yanke shawarar a fara tseratar da mu daga baya a zo a kwashe su marigayin.”
Ya kara da cewa, “A cikin jirgin mu uku ne maza da mata biyar da babura shida, kafin a kai mu gaba a dawo jirgin ya nutse da su, sauran sun tsira marigayi ne kadai ya nutse a ruwa sai da aka kwashe fiye da awa uku kafin a gano gawarsa.” Marigayin jami’i ne a kungiyar Jama’atul Nasril Islam baya ga aikin kiwon lafiya da yake yi.
A ranar Lahadi ne Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tabuwal ya kaddamar da shirin bayar da magungunan zazzabin maleriya a karamar hukumar ta Isa, inda ya ce, ana sa ran za a bai wa yara miliyan daya da dubu 800 maganin cutar maleriya a kokarin da gwamnatin ke yi na kawar da cutar a jihar. Ya ce gwamnati za ta dauki duk wani mataki na kawar da cutar da sauran cututtuka wanda hakan ne ya sanya ta giggina wuraren shan magani da kiwon lafiya a sassan jihar.
Ya ce a kokarin haka ne gwamnatinsa ta daukaka tare da gyara asibitocin Yabo da Dogon Daji da Silame da Illela kuma aikin ya kusa kammala.  Gwamna Tambuwal ya roki shugabannin kananan hukumomin jihar su bai wa aikin goyon baya domin samun nasara, kuma ya gode wa kungiyoyin sa-kai da ke taimaka wa aikin da kuma Majalisar Sarkin Musulmi da ke ba su hadin kai wajen tattaro wadanda za a bai wa maganin.