Ruwa ya ci mutum takwas a Akwa Ibom
Ruwa ya ci wasu yara su takwas ’yan makarantar firamare da ke kauyen Ikot Abia Enyia a karamar Hukumar Atai da ke Jihar Akwa Ibom. Kamar yadda labarin afkuwar hakan ya riski Aminiya daga bakin basaraken kauyen, Etop Umana, ya ce ruwan wani rafi ya cika ya tumbatsa sakamakon ruwan sama da aka yi kamar […]
Ruwa ya ci wasu yara su takwas ’yan makarantar firamare da ke kauyen Ikot Abia Enyia a karamar Hukumar Atai da ke Jihar Akwa Ibom.
Kamar yadda labarin afkuwar hakan ya riski Aminiya daga bakin basaraken kauyen, Etop Umana, ya ce ruwan wani rafi ya cika ya tumbatsa sakamakon ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya.
Ya ce ruwan ya shafe hanya, sai karar kwana ta kawo wadannan yara da suka taso makaranta, a kokarin da suke yi na ketare kogin. Mutane sun bazama cikin koramar ana neman gawarwakin yaran, har sai da aka shafe kwana uku ana nema kafin daga bisani a gano gawarsu.
An tabbatar wa wannan jarida cewa ko a shekarar da ta gabata ma sai da ruwan ya ci yara uku da wata mace mai dauke da juna biyu. “kauyen daya ne, wannan korama ce kadai da ta raba kauyen gida biyu kuma a wancan tsallake ne aka yi makaranta da kuma dakin shan magani. Babu yadda za a yi a ce a yanke mu’amala.”
Daga bisani Kwamishina mai kula da harkokin raya karkara, Ekong Sampson ya bayyana takaicin gwamnati na asarar rayuka da kowace shekara ake samu a wannan korama. Ya ce gwamnati za ta kawo dauki domin magance hakan. Za a dauki matakin fitar da hanyoyi cikin kauyen da kuma gina gada domin a ji dadin tsallake koramar.