Ruwa ya ci su a kokarin guje wa mahara
Kananan yara da mata na cikin mutanen da suka nitse a ruwa a Jihar Neja
Akalla mutum biyar ne suka nitse a kwalekwale a rafin Gurmana da ke Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
Mutanen da kwalekwalensu ya nitse da su din sun hada da mata uku da kananan yara biyu.
Rahotanni sun ce mutanen sun hadu da ajalinsu bayan sun samu labarin mahara sun kai hari a kauyukan da ke makwabtaka da su, inda suka yanke shawarar hawa kwalekwalen domin su tsira da rayuwarsu.
Jagoran wata kungiyar matasa a karamar hukumar, Sani Abubakar Kokki ya ce mazauna kauyukan dama kan hau kwalekwale domin guduwa idan suka ji ‘yan bindiga za su kawo hari.
Ya kuma ce jirgin nasu ya kife ne suna dab da kaiwa masaukinsu.
“Hadarin ya faru ne da daren Alhamis lokacin da wani jirgi dauke da mutane ya kife kuma wasu daga cikin fasinjojinsa suka nitse.
“Ko a kwanakin baya ma makamancin wannan hastarin ya faru lokacin da mutane ke kokarin guje wa mahara, a kan samu asarar rayuka da dama ta sanadin haka”, inji Sani.
Ya ce tuni mutane masu aikin sa kai suka dukufa neman gawarwakin da suka nitse a ruwan, ko da yake ya zuwa yanzu ba a sami tsamo ko da mutum daya daga cikin biyar din da suka halaka ba.
Babban daraktan hukumar ba da agaji ta jihar Neja (SEMA), Ibrahim Ahmad Inga ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an fara kokarin tsamo mutanen da suka nitse.