Ruwa ya ci wadanda suka fito zikiri a Sakkwato

A ranar Alhamis din makon jiya ne al’ummar kauyen Ballah a ke karamar Hukumar Goronyo a Jihar Sakkwato suka yi alhinin rasa ’ya’yansu 15 dukkansu samari a hadarin mota da ya faru a garin Taloka a hanyarsu ta dawowa daga majalisin Zikiri. Aminiya ta ziyarci kauyen inda ta zanta da daya daga cikin mutum biyu […]

Ruwa ya ci wadanda suka fito zikiri a Sakkwato
Ruwa ya ci wadanda suka fito zikiri a Sakkwato

A ranar Alhamis din makon jiya ne al’ummar kauyen Ballah a ke karamar Hukumar Goronyo a Jihar Sakkwato suka yi alhinin rasa ’ya’yansu 15 dukkansu samari a hadarin mota da ya faru a garin Taloka a hanyarsu ta dawowa daga majalisin Zikiri.

Aminiya ta ziyarci kauyen inda ta zanta da daya daga cikin mutum biyu da suka kubuta daga hadarin, mai suna Shehu Mai Kasuwa wanda ya ce “Hadarin ya same mu ne a hanyarmu ta dawowa daga wurin Zikiri, daga fitowarmu garin ko kilomita daya ba mu ci ba, motar ta kwace wa direbanmu muka fada madatsar ruwa ta garin Kanal ta rika juyawa damu cikin ruwa kusan sau uku, daga nan ne na ganni a waje bayan motar ta birkice samanta ya dawo kasa.”
Ya ce, shi da Muddaha da suka tsira, sun rika kuwwar neman agaji inda wasu mutane suka zo amma ba su shiga ba don ba su iya ruwa ba, haka suka tsaya har mutanen garin Taloka suka fito da igiyoyi domin taimaka musu, wasu suka shiga ruwan aka daura igiya a jikin mota aka samu aka fito da mutanen daga cikin ruwan, ya duba su da kansa ba mai motsi duk sun rasu.
Malam Shehu ya ce “Abin da ya fi daga min hankali, direbanmu a hankali yake tafiya, ina gaba duk da dare ya tsala saboda mun baro garin ne karfe 2:00 na dare, sai kawai tsautsayi ya gitta mana, a rayuwata ban taba ganin rasuwar mutum 15 a lokaci guda ba,” inji shi.
Hakimin Ballah wanda ya wakilta Malam Usman Marafa ya yi magana a madadinsa kan rashin da suka yi da suka kira masifar da ba su taba ganin irinta ba, ya ce dukkan mutanen da ke cikin motar ’yan wannan gari ne matasa da dattawa, don haka mutuwar ta girgiza su.
Ya ce Gwamna Wamakko da Shugaban karamar Hukumar Goronyo, Alhaji Faruku Rimawa sun yi musu ta’aziyya. Alhaji Musa S. Adar ya zo ya yi gaisuwa tare da tallafin buhun shinkafa 17 da Naira dubu 10, wakilin Mataimakin Gwamna Mukhtari Shagari ya zo da Naira dubu 30 ga daya daga cikin mamatan a saya wa matarsa ragon suna don Asabar ne suna ya rasu ranar Alhamis.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi