Ruwa ya kare wa dan kada
Hausawa na cewa wankan wuta sau guda ake yafawa. Ilai kuwa ga haka nan yana son zama hakkun ga Shugaba Goodluck Ebele Jonathan, wanda a halin yanzu jama’ar Najeriya suka juya masa baya, kuma bisa ga dukkan alamu zai yi wuya ya sake komawa bisa kujerarsa ta shugabancin kasar nan bayan zaben watan Afrilu. Dalili […]
Hausawa na cewa wankan wuta sau guda ake yafawa. Ilai kuwa ga haka nan yana son zama hakkun ga Shugaba Goodluck Ebele Jonathan, wanda a halin yanzu jama’ar Najeriya suka juya masa baya, kuma bisa ga dukkan alamu zai yi wuya ya sake komawa bisa kujerarsa ta shugabancin kasar nan bayan zaben watan Afrilu. Dalili kuwa shi ne takobin da ya yi amfani da shi a shekarar 2011 da shi ne kuma ake yakarsa da shi, kuma zafin yankan da ake yi masa da wannan takobin ya fi na wanda ya yi wa talakawan kasar nan ciwo matuka. Wannan makamin kuwa shi ne batun addini, wanda uwargidansa, Dame Patience Jonathan ta wuce gaba wajen harhada kawunan limaman addinin Kirista na Kudanci da kuma wasu sassan Arewaci don hure wa mabiyansu kunnuwa, su kuma ba shi goyon baya a matsayinsa na dan uwansu mai bin addinin da suke bi.
Wannan abu ya yi tasiri ainun, domin kuwa sai da Dame Patience ta ja maigidanta, ta kai shi gaban wani limamin cocinsa na Angilikan, inda ya durkasa a gabansa yana neman tubarraki, daf da gabatowar zaben shugaban kasa na 2011. An dauki hoton Jonathan limamin na shafa kansa, yana yi masa addu’a, daga bisani kuma aka yi ta wanke kwafen wannan hoton, ana aikewa da shi coci-coci da wurare daban-daban don yakin neman zabe, a kuma nuna cewa shi Kirista ne na kwarai, wanda ya kamata dukkan mabiya addininsa su yi amanna da shi.
Ilai kuwa haka din aka yi, domin mabiyansa sun biye wa addini wajen zabensa, suka kuma yi amfani da bambancin addinin suka bakanta abokin adawarsa, Janar Muhamadu Buhari, sa’annan kuma sakamakon zaben ya nuna a zahiri yadda Kiristan Kudu da na Arewa suka gwammace dan uwansu Kirista, kuma Musulmin Arewacin kasar nan suka zurara wa dan uwansu Musulmi nasu kuri’un. Hakan ya raba kawunan mabiya addinan nan guda biyu, kuma bayan zaben 2011 sai aka shiga wani zamani na tsananin gaba da kiyayya tsakanin mabiya addinan, kuma shugabannin gwamnatin tarayya ba su boye kyamar da suke yi wa wadanda ba addininsu daya ba, suka mayar da addini shi ne a’ala a harkokin mulki.
Dangane da haka ne kasar ta fada cikin wani mummunan yanayi; ta’addanci ya gawurta, aka kasa maganinsa domin a kawo batun addini da kabilanci a ciki; rashawa da cin hanci suka gawurta, ba wani mai amfana daga harkokin gwamnati sai wanda ya zake wajen kishin addinin Shugaba Jonathan da kuma nuna kiyayya, muraran, ga addinin Musulunci da mabiyansa. Wannan ne ya ba Shugaba Jonathan da mukarrabansa daman mike kafa, suka shantake wajen amfani da addini don rarraba kawunan jama’a, musamman ma na Arewa don su ji dadin cin karensu ba babbaka.
Amma da yake an ce a dade ana yi sai gaskiya, sai ga shi nan ita gaskiyar ta yi halinta. Turbar da Shugaba Jonathan ya dauka, ko kuma a ce wacce mayaudara, masu ci da addini suka dora shi bisanta ce ta zame gajeruwa, ko ba ta wucewa ko’ina. Batun addinin da ya sanya a gaba ya rufe masa idanu, har ta kai idan ba ya-nasa-ya-nasa ba, ba ya mu’amala da kowa, sauran al’ummomin kasar nan kuwa ko oho. Wadanda ma suka tagayyara sakamakon bala’o’in da lusaranci suka hana shi kawarwa bai batunsu, ba kuma ruwansa da matsaloli ko wahalhalun da ke addabarsu, hasali ma shi batun zabensa ya fi masa muhimmanci fiye da yanayin rayuwarsu, domin kuwa tun lokacin da suka fara tagayyara bai bi ta kansu ba, bai kuma ziyarce su ya gane wa idanunsa halin da suke ciki ba, sai a yanzu ne da zabe ya karato yake son wanke kafarsa ya tafi wurarensu don yakin neman zabe. To idan ya je mai zai ce da su?
Sa’ilin da Shugaba Jonathan da jama’arsa suka hau dawakan zuciya, suna aikta masha’a yadda suke so, sun manta cewa idan kai ne yau, ba kai ne gobe ba. Sun dauka ke nan halin da suke ciki zai dore, har sai Mahdi ya zo, ya tarwatsa su. To tun kafin a kai ko’ina sai ga shi sun fara gamuwa da gamonsu, dan hakin da suka raina na neman ya tsokane masu ido. Haka nan kawai, bagatatan, sai ga shi nan jama’ar Jonathan sun farka, sun kuma farga cewa ashe dai ya kai su ne, ya baro a banza. Ya mayar da su kurayen da shi da makararrabansa, a matsayin gardawa, suka yi ta amfana daga kudin da ake samu bayan an yi wasa da su, sun sha jibga. Nan take suka sake dabara, suka fahimci irin kwarar da aka yi masu da yadda aka yi ta ci da guminsu, aka tura matacciyar mota tare da su, bayan ta tashi kuma sai aka tafi aka bar su. Abin takaici game da haka shi ne duk da sunan addini ne aka yaudare su, aka yi musu sakiyar da ba ruwa.
Shi ya sa a ‘yan kwanakin nan reshe ya juye da mujiya, jam’iyyar da suka mayar ‘yar bora sai ga shi nan ta yunkura, tana neman ta tunkude tasu daga bisa karaga, jama’a kuma sun raja’a gare ta, suna ta kwanzarta dan takararta, Janar Muhammadu Buhari wanda a shekaru hudu da suka wuce ba irin cin kashin da ba su yi masa ba.
Baicin haka nan kuma sai ga shi nan ‘yan kabilar Ibo da suka fi mai kora shafawa wajen nuna kiyayya ga Janar Muhammadu Buhari sun komo daga rakiyar Jonathan, wanda suka ce sun danne masa kan maciji ne yana ta wasa da wutsiyar a banza, ana ta gudanar da harkoki ba tare da su ba, inda aka mayar da shugabanninsu saniyar-ware.
To, sai ga shi nan wani babban Limamin wani cocin Katolika na garin Enugu, Rabaran Faza Ejike Mbaka, ya wanke wa Shugaba Jonathan hannu aka, ya bukace shi da ya janye daga takarar shugabancin kasa, ya bar wa Janar Muhamadu Buhari, domin kuwa ya zame wa Najeriya tauraro mai wutsiya, kuma dorewarsa bisa mulki babban masifa ce ga kasar. Hakan kuwa ya biyo bayan wadarin da Dame Patience ne ta yi ta zuwa coci-coci a kasar Inyamurai, amma inda duk ta je sai a duba mata, a ce sa’a ba ta tare da mijinta.
Yanzu dai daukacin al’ummomin Najeriya sun juya wa Jonathan baya, musamman ma wadanda suka yi amfani da addini don daure masa gindi a zaben 2011, kuma suna ji, suna gani, ba abin da suka iya yi tunda dai ruwa ya karewa dan kada, ga shi nan kuri!