Ruwa ya lalata gidaje dubu a Malam Madori
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka samu a wasu sassan Jihar Jigawa ya yi sanadin rugujewar fiye da gidaje dubu a yankin karamar Hukumar Malam Madori da ke jihar.Ruwan ya yi sanadin lalacewar hanyoyin sadarwa da wayoyin wutar lantarki yayin da itatuwa da dama suka fadi.Wuraren da ruwan ya fi yi wa gyara […]
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka samu a wasu sassan Jihar Jigawa ya yi sanadin rugujewar fiye da gidaje dubu a yankin karamar Hukumar Malam Madori da ke jihar.
Ruwan ya yi sanadin lalacewar hanyoyin sadarwa da wayoyin wutar lantarki yayin da itatuwa da dama suka fadi.
Wuraren da ruwan ya fi yi wa gyara sun hada da Unguwar Dunari da Sirinya da Kamfala da kuma Unguwar Sabon Garin Malam Madori da Tasha Garin Dokajo.
Yanzu haka mutane da dama da lamarin ya shafa suna kwana a makarantun gwamnati da gidajan ’yan uwa da asibitoci da sauran gine-ginen gwamnati ne, yayin da wasu suka koma kwana a dakunan kara da bukkokin ciyawa.
Shugaban karamar hukumar Alhaji Haruna Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce karamar hukumar ta nada kwamatin bayar da agajin gaggawa don tallafa wa mutanen da abin ya shafa.
Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa Alhaji Aliyu Ibrahim Waziri ya ce sama da gidaje dubu ne suka ruguje a garin Malam Madori kuma jama’a suna bukatar agajin gaggawa. Ya ce tuni hukumarsa ta tura kwararru domin tantance wadanda abin ya shafa da nufin taimaka musu “nan ba da dadewa ba za a kai kayan agaji garin,” inji shi.
Sakataren ya ce gwamnatin jihar ta kafa wani kwamatin tantancewa a karkashin ofishin Mataimakin Gwamnan Jihar da nufin agaza wa wadanda abin ya shafa.