Ruwa ya nutse da yaro a Kano
Rahotanni daga jihar Kano na cewa, ruwa ya nutse da wani yaro mai suna, Huzaifa Abdulrashid, mai shekara 14 lokacin da yake wanka a wani tafki da ke hanyar Gwarzo da ke karamar hukumar Gwale ta jihar. Kakakin hukumar kashe gobara na jihar Kano Saidu Mohammed ne bayyanawa Kamfanin Dillancin Labarai NAN aukuwar hakan a […]
Rahotanni daga jihar Kano na cewa, ruwa ya nutse da wani yaro mai suna, Huzaifa Abdulrashid, mai shekara 14 lokacin da yake wanka a wani tafki da ke hanyar Gwarzo da ke karamar hukumar Gwale ta jihar.
Kakakin hukumar kashe gobara na jihar Kano Saidu Mohammed ne bayyanawa Kamfanin Dillancin Labarai NAN aukuwar hakan a yau Juma’a .
Saidu, ya ce sun samu sanarwa ta hanyar kiran waya daga Malam Habibu Ibrahim da misalin karfe 07:35 na safe cewa, an ga Huzaifa a saman ruwa. Hakan yasa muka tura jami’an mu don ceton yaron.