Ruwa ya raba sama da mutum 3000 da muhallinsu a Kebbi
Sama da mutum dubu uku ne suka rasa muhallinsu a garin Makirim da ke karama Hukumar Ngaski a Jihar Kebbi, sanadiyar ruwan sama da iska da aka kwashe sa’o’i kusan biyar ana shekawa a yankin.Al’ummar garin Makirin da suke cike da juyayi kan yadda ruwa da iska suka yi gaba da gidaje da dukiyoyinsu sun […]
Sama da mutum dubu uku ne suka rasa muhallinsu a garin Makirim da ke karama Hukumar Ngaski a Jihar Kebbi, sanadiyar ruwan sama da iska da aka kwashe sa’o’i kusan biyar ana shekawa a yankin.
Al’ummar garin Makirin da suke cike da juyayi kan yadda ruwa da iska suka yi gaba da gidaje da dukiyoyinsu sun ce an fara tafka ruwan ne tun cikin dare har zuwa wayewar gari.
Binciken da wakilinmu ya gudanar a kauyen ya gano cewa mutum biyu sun rasa rayukansu a cikin lamarin, yayin da kimanin gidaje 200 suka rushe, baya ga makarantu da masallatai da asibitoci da sauran gine-ginen gwamnati da kuma turakun wutar lantarki da aka kafa su tun lokacin marigayi Sardauna.
Kantoman karamar Hukumar Ngaski, Alhaji Shehu Barau Ngaski ya jajenta wa al’ummar yanki, inda ya wannan ruwa da iska da suka yi sanadiyyar asarar dukiyoyin jama’a da daruruwan gidaje da kayayyakin abinci, wadansu manyan masifu ne.
Alhaji Shehu Barau ya yi addu’ar Allah Ya tsayar da wannan masifa hala tare da addu’ar wadanda suka rasa dukiyoyi da gidajensu Allah Ya mayar musu da alheri.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kebbi da masu hannu da shuni su taimaka wa wadanda lamarin ya shafa.