Ruwa ya rusa gidaje 100 a Damaturu
Ruwan sama kamar da bakin kwarya dauke da iska mai karfi da aka yi a garin Damaturu fadar Jihar Yobe ya yi sanadiyar rasuwar mutum daya da ji wa mutane da dama raunuka tare da rushe gidaje sama da 100 da salwanta dukiya ta milyoyin Naira.Aminiya ta gano ruwan da aka fara da yamma inda […]
Ruwan sama kamar da bakin kwarya dauke da iska mai karfi da aka yi a garin Damaturu fadar Jihar Yobe ya yi sanadiyar rasuwar mutum daya da ji wa mutane da dama raunuka tare da rushe gidaje sama da 100 da salwanta dukiya ta milyoyin Naira.
Aminiya ta gano ruwan da aka fara da yamma inda aka shafe sama da awa biyu ana sheka shi hade da iska mai karfi ya haifar da jikkatar jama’a da dama saboda an kai dare ana yin sa ba tare da kakkautawa ba, sai da jami’an tsaro na JTF suka rika kai dauki ga wasu mutane da suna kai wadanda suka samu raunuka asibiti.
Unguwannin Nayi-Naywa da Unguwar Wan Miliyon Road da Nai-Nawa Sabuwar Gada da wasu bangarori na Unguwar Hausari da sauransu ne ruwan ya fi yi wa gyara, inda gidaje da shaguna masu yawa da dukiya mai suka salwanta, yayin da jama’a suka samu raunukan da suka hada da karaya, sannan wani daki ya fada a kan wata mace ta rasu.
Malam Musa Muhammad na Unguwar Nayi-Naya da Malam Isiyaku Idrisa sun ce dakunansu sun rushe, kuma sun rasa kusan dukan kayayyakin da suka mallaka.
Malam Alhassan Sulaiman da Musa Mai Kayan-Koli sun shaida wa Aminiya ce lokacin da aka fara sheka ruwan tun farko gidajensu suka rushe daga bisani kuma iska ta yi awon gaba da rufin dakunansu zuwa wasu wuraren da ba su iya gano su ba. Sai suka roki gwamnatin Jihar Yobe ta gaggauta kai musu dauki saboda su da iyalansu suna bukatar tallafin gaggawa.
Shugaban karamar Hukumar Damaturu Alhaji Kale Muhammad ya ce suna kokarin sanar da Hukumar Bada Tallafin Gaggawa ta Jihar (SERA) don kai dauki cikin lokaci ga al’ummar, yayin da karamar hukumar ke nazarin abin da ya kamata ta yi cikin lokaci.
Kwamshinan Muhalli na Jihar Alhaji Idi Barde Gubana ya ce matsalar ambaliyar ba ta da nasaba da rashin wadatattun magudanun ruwa garin Damaturu, inda ya ce a kusan ilahirin garin, gwamnati ta samar da magudanun ruwa, haka ma a wasu manyan biranen jihar irin su Potiskum da Gashuwa da Nguru da Gaidam.