Ruwa ya rushe sama da gidaje 200 a Jigawa

Ruwan sama mai kamar da bakin kwarya ya rushe kimanin gidaje 200 a sassan Jihar Jigawa, lamarin da ya sa daruruwan jama’a a kananan hukumomin Taura da Ringim da Hadeja cikin mawuyacin hali. Gwamnatin jihar ta ce an samu asarar kayayyaki masu yawa ciki har da kayan Wakilin Aminiya ya ziyarci Ringim da Taura da […]

Ruwa ya rushe sama da gidaje 200 a Jigawa
Ruwa ya rushe sama da gidaje 200 a Jigawa

Ruwan sama mai kamar da bakin kwarya ya rushe kimanin gidaje 200 a sassan Jihar Jigawa, lamarin da ya sa daruruwan jama’a a kananan hukumomin Taura da Ringim da Hadeja cikin mawuyacin hali. Gwamnatin jihar ta ce an samu asarar kayayyaki masu yawa ciki har da kayan Wakilin Aminiya ya ziyarci Ringim da Taura da Hadeja, inda ya ga daruruwan mutane zazzune a gindin bishiyoyi yayin da wasu suke tsugunne a kofar gidajen makwabta. A karamar Hukumar Ringim wadanda ruwan ya raba da mahallinsu na tsugune ne a wata makaranta, inda wani mai suna Malam Nuhu Tanimu ya ce karamar Hukumar Ringim ta samar musu da rumfunan wucin-gadi a firamaren Ringim. Malam Tanimu ya ce rashin magudanun ruwa ne ya sa gidajensu suka rushe saboda mafiyansu na laka ne. A Taura wanda ya yi magana a madadin jama’ar da ambaliyar ta shafa Malam Usman Muhammed Taura ya ce akwai karancin magudanun ruwa a garin, inda ya ce rabonsu da magudanar ruwa tun wadda aka gina zamanin Gwamna Ali Sa’adu Birnin Kudu. Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido ya kafa wani kwamitin taimaka wa wadanda gidajansu suka lalace tare da nemo hanyar magance matsalar ambaliyar. ’Yan kwamitin a karkashin shugabancin Kwamashinan Ruwa Alhaji Jinjiri Dutse wakilansa sun hada da Kwamishinan Lafiya da na Ilimi da na Muhalli da na Raya Karkara.