Ruwan Bama-Bamai A Arewa: Gari Na Dada Wayewa
Komai nisan dare, inji Hausawa, gari zai waye. Duk kuma yadda aka kai ga yada karya da karairayi, kuma duk yadda aka ki gaskiya, aka guje mata, watan wata rana sai ta bayyana, ko ana so kuma ko ba a so! A yau Kusan tsawon shekara hudu ke nan ana abu daya, ana dasa bama-bamai […]
Komai nisan dare, inji Hausawa, gari zai waye. Duk kuma yadda aka kai ga yada karya da karairayi, kuma duk yadda aka ki gaskiya, aka guje mata, watan wata rana sai ta bayyana, ko ana so kuma ko ba a so! A yau Kusan tsawon shekara hudu ke nan ana abu daya, ana dasa bama-bamai a yankunan Arewacin Najeriya, inda aka assasa ko ake ta ci gaba da tafka barnar rayuka da dukiyoyin al’umma ba adadi.
Duk wani ta’annati da ake yi a sanadiyyar yaki, babu wanda ba a yi wa al’ummar arewa ba. An kasha al’umma, wadanda suka hada da shugabanni, sarakuna, tsoffi da mata da yara. An yi sace-sace da barnata dukiya. An ci zarafin mata, ta yi masu fyade das ace su bisa tilas. An kassara makarantu da cibiyoyin ilimi. An fasa kasuwa, an fasa bankuna, an fasa barikokin soja da na ‘’yan sanda, kamar kuma yadda aka fasa gidajen yari daban-daban. An dasa bama-bamai a masallatai da majami’u. a halin da ake ciki, babu wani ma’auni da za a iya amfani das hi wajen kididdige iya ta’adin da aka yi wa al’umma ko kuma ma mu ce ake ci gaba da yi wa al’umma.
Tun da aka fara want ton bahallatsa mai sunan Boko Hara make ta baza karya da karairayi, wadanda za mu alakanta da bakin dare mai tsananin duhu, duhun da a kullum haske ke neman cin masa, domin kuwa a lokacin da duhun ke kara bayyana, hasken gari kuma yana dada wayewa ne. a lokacin da ake ta baza karairayin, sai gas hi gaskiya na sarkakowa, tana ta bayyana, al’umma na kara fahimtar inda aka dosa.
Tun da farko, ‘’yan Boko Haram da wasu majibintansu suna baza karyar cewa wai jihadi suke yi, suna kokarin tsarkake al’umma, wai a nufinsu na musuluntar da najeriya da al’ummarta. Tuni want ton karyar ta zama karya tantagaryarta, inda gaskiya tam aye gurbinta. Gaskiyar it ace, babu wani jihadi da suke yi, domin kuwa babu wani littafin Allah ko zancen Annabi Muhammad (SAW) da ya nuna cewa za ka tilasta wa mutum ya amshi addininka don dole. Haka kuma babu inda aka ce kai tsaye za ka rika kasha al’umma da nufin tsorata su don su shiga addininka. karin karau, sai gas hi kuma kididdiga ta tabbatar da cewa al’ummar Musulmi su aka fi kashewa, su aka fi tagayyarawa, su aka fi lalata wa dukiya. Hasali ma, a yankinsu aka yi tunga, aka hana su rawar gaban hantsi. Ta yaya za ka yi jihadi kuma kana kasha mabiya addinin da kake son jaddadawa? Lallai gari y agama wayewa a nan, sai dai a fadi wani abun kuma!
Wata karya kuma da ta yi tashe ko kuma take tashe har yanzu it ace, yadda aka alakanta al’amarin nan da makircin siyasa. Wasu mukarraban gwamnatin da ke ci a yanzu, wato magoya bayan Shugaban kasa Goodluck Jonathan sun kafe da cewa wai wasu ‘’yan Arewa ne suka assasa Boko Haram da nufin dakile ko kuma kawo wa mulkin Jonathan cikas. Tuni want ton duhun y agama tashe, tuni hasken lamarin ya bayyana kuma al’umma suka gano cewa want ton balulluba ce kawai.
Idan har gaskiya ne cewa wasu ‘’yan soyasar Arewa ne suka assasa Boko Haram don su dakile Gwamnatin Jonathan, to ita gwamnatin wane mataki ta dauka na fallasa su da dakile su? Ko kuwa gwamnatin na nufin wasu tsiraru sun fiu karfinta ne? batun bah aka yake ba, domin kuwa tashin farko idan za mu yi tambaya, kafin Boko Haram su fara tada bom, su wa suka fara? Su Henry Okah ne, mutanen da suka fito yanki daya das hi Shugaban kasa Jonathan. Na biyu, shi kansa Shugaban Jonathan ya taba furtawa da bakinsa cewa gwamnatinsa cike take da ‘’yan Boko Haram. Na uku, marigayi Hafsan Hafsoshin tsaro a Gwamnatin Jonthan ya taba furta cewa gwamnatin PDP it ace Boko Haram. Na hudu, tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya yi rubutu mai tsawo, inda ya bayyana cewa lallai akwai shiri na musamman da gwamnatin Jonathan ta yi, inda ta ware wasu zaratan matasa, ana koya masu yadda za su aiwatar da kasha-kashen wasu muhimman mutane. Duk da cewa an karyata want ton batu nasa, amma kuma an samu sakamako mai kama da wnnan, inda aka halaka wasu muhimman malaman addinin Musulunci, kamar Shaikh albani. Haka ma wasu suka shiga suka halaka marigayi Mamman Shuwa, gas hi kuma an kasha ‘’yan’yan Shaikh Alzakzaky har su uku. tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Murtala Nyako shi ma ya yi wani dogon nazari, inda ya bayyana karara cewa lallai gwamnatin Jonathan na da hannu cikin want ton batu na kasha-kashen al’umma a Arewa. Duk da an karyata, amma abin da ke daure kais hi ne, yadda gwamnatin ke yi wa al’amura tsaro rikon sakainar kasha. Me ya sanya haka? Tambayar da take da wuyar amsawa ken an amma kuma tana kara wa bayanin Obasanjo da Nyako karfi.
Wasu tambayoyi da suka kara gagarar amsawa, wadanda kuma ke kara haske da ke korar duhun karairayin da ake yadawa game da Boko Haram su ne: Me ya sa sai a Arewa ne ake tayar da boma-bomai? Me ya sa kuma sai a jihohin adawa, kamar Borno, Yobe, Kano ne al’amarin ya yi kamari? Wata tambaya ma mai daura kai it ace, me ya sa har zuwa yau din nan Shugaba Jonathan bay a ziyartar jihohin da ake kasha-kashen nan? Ko makon day a gabata, an dasa bom a babban masallacin Juma’a na Kano, inda mutane sama da dariu suka halaka, amma Joanathan bai je ba, sai dai ya tura Mataimakinsa Namadi Sambo. Amma sai gas hi a kwanakin baya Shugaba Jonathan ya kai ziyarar nuna alhini Legas, inda Cocin Fato T. B. Joshua ya rushe, ya halaka mutane. Me want ton yake nunawa ga mai hankali? Me ya sanya da zarar an nsamu wani dalili na fallasa gwamnati sai ka ga ana ta kai hare-haren bom a Arewa? Wasu na nuna cewa lallai ana son dauke hankalin jama’a ne daga ainahin gaskiya.
Haka kuma, ina muwarraban Jonathan, irinsu Asari Dokubo? Me suka taba cewa game da shugaban? Asari Dokubo ya taba fadin cewa za su tayar da zaune tsayte, muddin ba a sake zaben shuagban a karo na biyu ba. A kwanakin baya, sau biyu ana kama jiragen sama a kasar Afirika ta Kudu, daya jirgin ma mallakar Shugbanan kungiyar Kiristoci Ta Najeriya, Fasto Oritesjafor ne. An kama jirgin da kudi masu yawa kuma an samu tabbacin cewa makamai za a sawo ta barauniyar hanya. Shin me hakan ke nunawa?
Wani abin da zai kara ba ka mamaki game da gwamnatin nan shi ne, yadda jami’an tsaro, musamman sojan Najeriya suka sukurkuce. Sojojin nan sun samu tarihin jaruntaka a kasashe da daman a duniya, amma sai a gida ne wata ‘karamar kungiya’ za ta gagare su? An yi kukan cewa bas u da ingantattun kayan aiki. To ina makudan kudin da ake kasafta wa harkar tsaro kowace shekara?
Ga wani babban kalubalen kuma: Mafi yawan jiga-jigan hukumomin tsaro duk ‘’yan Arewa ne, kama daga Ministan tsaro da mai ba shugaba shawara ta fuskar tsaro da sufeto janar na ‘’yan sanda da shugaban kwastan da hafsan-hafsoshin soja da sauransu da dama. Shin me wadannan mutane suka tsinanna, a lokacin da yankunansu ke cikin ukubar kasha-kashe da lalata dukiya?
Babu shakka an dade ana tafka dare, amma gari ya fara wayewa, yana ma dada wayewa! An dade ana karya da karairayi, amma daga dukkan alamu gaskiya ta bayyana, karya kuwa za ta gushed a yardarm Allah. Allah Ka kawo mana dauki, ba don halayenmu da ayyukanmu ba, sai domin jinkanKa da izzar mulkinKa!