‘Ruwan harsasai aka yi wa Sankara’
A ranar Talatar da ta gabata ne Lauyan iyalan tsohon Shugaban kasar Burkina Faso, Thomas Sankara, ya ce binciken da aka gudanar a kan gawar marigayin ya nuna cewa an yi mata ruwan harsasai ne, kamar yadda kafar yada labarai na BBC ta bayyana.Lauyan ya kara da cewa har yanzu iyalan na jiran gwajin da […]
A ranar Talatar da ta gabata ne Lauyan iyalan tsohon Shugaban kasar Burkina Faso, Thomas Sankara, ya ce binciken da aka gudanar a kan gawar marigayin ya nuna cewa an yi mata ruwan harsasai ne, kamar yadda kafar yada labarai na BBC ta bayyana.
Lauyan ya kara da cewa har yanzu iyalan na jiran gwajin da zai tabbatar masu da cewa gawar tasa ce.
An yi hanzarin binne marigayi ne, wanda aka yi wa lakabi da ‘Che Guebara’, bayan juyin mulkin da aka yi a kasar a shekarar 1987.
Ba a bayar da damar tono gawar ba a shekaru 27 da Shugaba Blaise Compaore, tsohon shugaban da aka hambarar a wata tarzoma a shekarar da ta gabata, ya kwashe yana mulki.
Mista Compaore ya jima yana musanta zargin da ake masa cewa yana da hannu a kisan da aka yi wa Sankara, inda yake ta nanata cewa komai a fili yake kuma ba shi da wani abu da yake boyewa, duk da cewar lokacin da yake mulki kotu ta toshe duk wata hanya ta yunkurin da iyalan Sankara suka yi domin a tono gawar.
Ambroise Farama, da ya daga cikin lauyoyin iyalan Sankara, ya ce abubuwan da aka gano a binciken gawar na da ban mamaki kwarai da gaske.