Ruwan sama da kankara ya lalata gonaki 300 a Katsina

A cikin ’yan mintoci ruwan sama da kankara ya lalata rufin gidaje tare da farfasa gialsan motoci da dama

Ruwan sama da kankara ya lalata gonaki 300 a Katsina

Wata gona da ruwan sama ya lalata

Amfanin gona sun lalace a gonaki akalla 300 sunnan rufin gidaje da dama sun lalace a sakamakon ruwan sama da kankara a Karamar Hukumar Kafur ta Jihar Katsina.

Shugaban Karamar Hukumar Kafur, Garba Kanya, ya ce an yi asarar miliyoyin Naira a kogani sama da 300 da ke daf da girbe shinkafa, masara, gero, shinkafa, waken suya, albasa da barkono, a yankin.

Wani mazaunin kauyen Gozaki, Malam Abdullahi Gozaki, ya ce ba su taba ganin irin ruwan sama da kankara haka ba.

Ya bayyana cewa a cikin ’yan mintoci ruwan da kankara ya lakata gonaki da rufin gidaje tare da farfasa gialsan motoci da dama.

Malam Abdullahi ya ce sauran unguwannin da aka samu hakan su ne Dutsen-Kura/Kanya  da Gozaki Gidan Danwada da kuma Gidan Sabo.

Sauran su ne; Kabalawa, Unguwar Tsamiya, Dandabo, Unguwar Maigarma, Unguwar Wanzamai da kuma Unguwar Fulani.

Shugaban Karamar Hukumar Kafur, Garba Kanya, ya ce sun sanar da Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Katsina da Hukumar Raya Karkara da sauran hukumomin da suka dace kuma sun zo sun gudanar da aikin tantance irin asara da aka yi.