Ruwan sama ya karya gadar da ta hada Bauchi da Gombe
Gwamnan Bauchi ya ce za a gyara ta a cikin mako guda
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi alkawarin bayar da duk tallafin da ake bukata domin a gyara gadar da ta karye a hanyar da ta hada jihohin Bauchi da Gombe a cikin mako guda.
Gwamna Bala ya yi wannan alkawarin ne a kauyen Kalajanga da ke Karamar Hukumar Kirfi a yau Lahadi lokacin da ya kai ziyarar tantance irin yankewar da hanyar ta yi sakamakon mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi da ya karya gadar.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ke Hana Matasan Najeriya Cigaba
- Abba Gida-Gida ya sake bude Asibitin Hasiya Bayero
Sai ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sake duba aikin gyaran hanyar Bauchi zuwa Gombe zuwa Taraba da aka bayar tun a shekarar 2018.
Gwamnan ya ce halin da hanyar ke ciki a yanzu yana da ban tsoro musamman yanda ya jefa al’umma halin kunci, sai ya yi kira da gwamnatin tarayya ta gaggauta kawo dauki.
Ya ce hanyar ta hada shiyyoyin kasar nan guda uku na Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, don haka akwai bukatar a gyara ta domin rage yawan mace-mace da hadurran da ke faruwa a kan ta.
Gwamnan ya yi kira ga masu ababen hawa da ’yan kasa da su yi hakuri, tare da yin alkawarin kawo musu dauki ta hanyar hada kai da hukumomin da abin ya shafa domin dakile illolin da rashin ta zai haifar.
Ya umurci babban Injiniya na jihar ya koma Kalajanga ya tabbatar da cewa ’yan kwangila sun bude hanyar cikin mako guda.
Ya ce alkawarin da dan kwangilar ya yi na gyara hanyar cikin kwanaki uku domin mai mota ya wuce ya ba shi kwarin gwiwa, ya kuma yi alkawarin mika wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima bukatar gyaran.
Dan kwangilar da ke kula da aikin, Injiniya Abraham ya yi alkawarin gyara hanyar cikin kwanaki uku, inda ya ce suna da isassun ma’aikata da injunan tabbatar da hakan.
Hakimin Kirfi, Alhaji Muhammad Lawal ya gode wa Gwamnan saboda ziyarar gaggawar da ya kai wa al’umma domin jajanta musu.