Ruwan sama ya lalata gidaje 100 a Filato
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya lalata gidaje sama da 100 a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu a Jihar Filato.
Mamakon ruwan sama da sanyin safiyar Alhamis ya lalata gidaje sama da 100 a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu a Jihar Filato.
Mazauna garin sun bayyana cewa ruwan sama da aka fara da misalin karfe 1 na dare, ya dauki kimanin sa’o’i uku.
Hakazalika ruwan na dauke da iska mai karfi da ta lalata rufin gidaje da dama, lamarin da ya sa iyalai da dama suka rasa matsugunansu.
Unguwanni da dama da suka hada da Jenta Adamu, Kabong, Angwan Rogo da mahadar Zololo na daga cikin wadanda guguwar ta shafa sosai.
- Mutane 30 sun mutu a harin ’yan ta’addan Katsina
- Yadda Sallar Layya za ta kasance a Najeriya da Saudiyya
- An kashe sama da mutane 100 a harin ƙauyen Sudan—Kwamitin
Emmanuel Ajang, daya daga cikin mutanen da lamarin ya shafa, ya bayyana lamarin a matsayin ma razanarwa, kuma ya raba iyalansa da matsuguninsu.
Shi ma wani mazauni mai suna Ibrahim Musa ya ce guguwar ta dauke kofar gidansa.