Ruwan sama ya rusa gidaje 150 a Dutse
Ruwan sama cike da iska mai karfin gaske ya rusa gidaje kusan 150 a Dutse fadar Jihar Jigawa inda ya yi sanadin rasuwar wani matashi a Unguwar Limawa da ke karamar Hukumar Dutse yayin da mutane da dama suka samu raunukan da aka kwantar da wasu a Asibitin danmasara da ke Dutse.Wakilinmu ya ce wuraren […]

Ruwan sama cike da iska mai karfin gaske ya rusa gidaje kusan 150 a Dutse fadar Jihar Jigawa inda ya yi sanadin rasuwar wani matashi a Unguwar Limawa da ke karamar Hukumar Dutse yayin da mutane da dama suka samu raunukan da aka kwantar da wasu a Asibitin danmasara da ke Dutse.
Wakilinmu ya ce wuraren da ruwan ya fi barna sun hada da kauyukan Galamawa da ketare da Kargo, inda a kauyen Kargo gini ya rubta wa wata mata da wani matashi ya karya su a cinya, kuma gidaje sama da 50 suka rushe.
Kamar yadda bayanai suka nuna sama da gidaje 100 suka salwanta a kauyukan Limawa da Galamawa da Unguwar ketare.
Wani da ya rasa gidansa a Unguwar Limawa mai suna Malam Rabi’u ya ce tunda yake bai taba ganin ruwa da iskar da suka yi wa jama’a barna kamar wannan ba.
Malam Rabi’u ya kara da cewa kusan duk gidajen da ke Unguwar Limawa ba gidan da iska ba ta yi wa barna ba, kuma lamarin ya jefa mazauna yankin a cikin halin damuwa.
Wani dan siyasa mazaunin yankin Alhaji Murtala Isah Galamawa ya ce mutanen yankin sun yi lissafi sama da gidaje 100 suka salwanta.
A lokacin da wakilimmu ya tuntubi jami’in hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Jigawa Malam Aminu B. Waziri ta waya bai same shi ba Amma kakakin rundunar ’yan sandan jihar DSP Audu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce iska mai karfi da ruwan sama sun salwantar da gidaje masu yawa a yankin Dutse.
Wata majiya ta ce Shugaban karamar Hukumar Dutse ya ziyarci wuraren da iska da
ruwan suka yi barna ya jajanta musu a kan lamarin har an ce wai ya sa an dauki sunayen magidantan da lamarin ya shafa da nufin gwamnatin jihar za ta taimaka musu a nan gaba.