Ruwan sama ya rushe gidaje sama da 4,500 a Birnin Kebbi
Sama da gidaje dubu hudu da dari biyar ne (4500) suka rushe a cikin garin Birnin Kebbi fadar Jihar Kebbi, sakamakon ruwan sama da iska da aka kwashe sa’o’i kusan bakwai ana shekawa a garin a ranar Talatar da ta gabata.Al’ummar Birnin Kebbi da suke cike da juyayin asarar kan dukiyoyinsu sun ce an fara […]
Sama da gidaje dubu hudu da dari biyar ne (4500) suka rushe a cikin garin Birnin Kebbi fadar Jihar Kebbi, sakamakon ruwan sama da iska da aka kwashe sa’o’i kusan bakwai ana shekawa a garin a ranar Talatar da ta gabata.
Al’ummar Birnin Kebbi da suke cike da juyayin asarar kan dukiyoyinsu sun ce an fara tafka ruwa ne tun da misalin karfe 4:45 na asuba har zuwa karfe 12:00 na rana.
Binciken da wakilinmu ya gudanar a cikin garin ya gano cewa babu wanda ya rasa ransa, illa dai yara guda biyu ne suka bata har zuwa lokacin turo labarinsa ba a gano su ba.
Wakilinmu ya zanta da wani magidanci mai suna El-Yakub Usman Dabai, inda ya ce babbar illar da ke kawo irin wannan rushewar gidaje idan an dade ana ruwan sama ita ce, yin gine-gine a kan hanyar ruwa da kuma zuba shara a cikin magudanun ruwa da jama’a ke yi.
A lokacin da yake zagayawa domin gane ea idonsa lamarin, Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya jajanta wa al’ummar garin, kan asarar dukiyoyin jama’a da dubban gidaje da kayayyakin abinci da dabbobi da kudi da suka yi inda ya bayyana hakan da wasu manyan masifu.
Gwamna Atiku Bagudu ya yi addu’ar Allah Ya tsayar da wannan masifa haka tare da addu’ar wadanda suka rasa dukiyoyi da gidajensu Allah Ya mayar musu da alheri, kuma nan take ya ba Kwamishinan Filaye da Gidaje iznin a rubuto sunayen wadanda abin ya shafa a unguwanni 12 da ruwa ya yi barna, domin duba yadda za a tallafa musu.
Ya roki jama’a su daina yin gine-gine a kan hanyar ruwa su kuma su guji zuba shara a cikin magudanun ruwa domin kauce wa irin wannan al’amari a nan gaba.