Ruwan sama ya shanye gidaje a Jalingo
Ruwan sama da aka samu na tsawon awa biyu ya sanya Kogin Mayo Gwoi ya yi ambaliya inda ruwan ya shanye gidade da dama.
Ambaliya
Ruwan sama ya shanye gidaje da dama a safiyar Litinin a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.
Ruwan sama da aka samu na tsawon awa biyu ya sanya Kogin Mayo Gwoi ya yi ambaliya inda ruwan ya shanye gidade da dama.
- ’Yan bindiga na neman N500m kan kwamishinar hukumar kidaya
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Jinkirin Kwaso ’Yan Najeriya Daga Sudan
Gidajen da ambaliyan ya rutsa da su, sun kasance ne a kan gabar kogin na Mayo Gwoi.
Duk da cewa babu asarar rai, amma dukiya da sauran kayan amfanin da ambaliyar ta lalata suna da matukar yawa.