Ruwan sama ya yi ajalin dattijuwa da jikarta, ya rushe gidaje a Bauchi
Rundunar ta ce za ta ci gaba da ƙoƙarin daƙile irin wannan iftila’i domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da rasuwar wata mata mai shekaru 50, Aisha Sagir da jikarta ’yar shekara huɗu, Aisha Shuaibu, sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da iska a ƙauyen Bara, da ke Ƙaramar Hukumar Kirfi.
Kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Laraba, 10 ga watan Yuni, 2026.
- Kano: Babu saki tsakanin masu auren gata sai da izinin Hisbah — Daurawa
- ’Yan bindiga sun kai hari makaranta, sun kashe malami tare da sace ɗalibai a Kogi
Rahotanni sun nuna cewa ruwan sama mai ƙarfi da iska ya yi ɓarna a yankin, inda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.
Baya ga mutuwar mutum biyu, ruwan saman ya rushe gidaje da dama, ya kashe dabbobi tare da lalata kayayyakin miliyoyin naira.
Jami’an ’yan sanda sun kai ziyara yankin da iftila’in ya faru domin tantance asara da kuma tabbatar da tsaro a yankin.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Sani-Omolori, ya yi alhini tare da ta’aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma al’ummar yankin.
Ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan mamatan, Ya kuma bai wa iyalansu haƙurin rashinsu.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar tare da haɗin gwiwar sauran hukumomi za su ci gaba da ƙoƙari wajen daƙile irin wannan iftila’i da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
Haka kuma ya yi kira ga mazauna Ƙaramar Hukumar Kirfi da su kasance cikin shiri a lokacin damina, tare da gaggauta kai rahoto ga hukumomi idan wani abu ya faru.
Wani shugaban al’umma a garin Bara, Alhaji Muhammad Bashir Bara Dan Galadiman Bara, ya ce al’ummar yankin sun tashi cikin alhini sakamakon iftila’in.