Ruwan sama: Yadda daminar 2022 za ta bambamta a Najeriya

Bayan saurin saukan ruwan sama, NIMET ta bayyana wa manoma abin da zai sa su ciza yatsa a daminar bana

Ruwan sama: Yadda daminar 2022 za ta bambamta a Najeriya

Saukar ruwan sama mai karfi

Damina na daya daga cikin nau’ukan yanayi da ake da su a Najeriya, a lokacin ne ruwan sama kan sauka har a samu amfanin gona.

A ’yan kwanakin da suka gabata an samu saukar ruwan sama a sassa daban-daban na Arewacin Najeriya kamar jihohin Kaduna, Katsina da dai sauransu.

Hatta a Maiduguri, Jihar Borno, inda ruwan sama bai saba sauka da wuri ba, an samu ruwa mai yawan gaske, inda aka shafe kusan awa guda ana ruwa kamar da bakin kwarya tare da iska mai karfi.

Sai dai idan za a iya tuna, hasashen daminar 2022 da Hukumar kula da Hasashen Yanayi ta Kasa (NIMET) ta fitar a baya, ya nuna a bana za a samu saurin saukar ruwan sama, amma ta shawarci manoma da kada su kuskura su fara shuka da wuri, domin saukar ruwan ba ya nufin damunar ta zauna.

Ganin cewa an shafe kwanaki ana ruwan sama, musamman a sassan Arewacin Najeriya, Aminya ta tuntubi hukumar inda muka tattauna da kakakin hukumar, Mista Adam James, domin samun karin hakse, kan dalilin hana manoma shuka, alhali sai kara samun ruwa ake yi a wurare daban-daban.

Mista Adam James ya bayyana cewa hasashen daminar da hukumar ta fitar a watan Fabrairu ya nuna za a iya samun ruwan sama a watannin Afrilu da Mayu, musamman a Arewacin Najeriya.

Sai dai kuma, tabbas bayan dan lokaci ruwan zai sake yankewa, wanda hakan kan iya haifar da asarar iri idan har manoma suka kuskura suka fara shuka da saukar wannan ruwan saman da suke gani a yanzu.

Kamar yadda NIMET ta bayyana, irin wannan ruwan sama da aka yi ta samu a Arewa,  ba ya nufin damina ta zauna, hasali ma ruwan zai sake yankewa har na tsawon mako uku zuwa hudu bai sake dawowa ba.

Kawo yanzu dai ana iya cewa hasashen saurin saukar ruwan ya tabbata, abin da ya rage shi ne na yankewarsa da aka yi hasashe.

Sai dai kuma shin manoma za su yi amafani da shawarar hukumar ta cewa kar su yi shuka da wuri domin kauce wa asara? Lokaci ne kadai ya nuna.

Yawan ruwan sama a daminar 2022

Game da yawan ruwan da za a samu a daminar bana kuwa, Mista James ya ce, a wannan shekarar za a samu ruwan sama sosai fiye da bara, da ma sauran shekarun da suka gabata, kamar yadda hasashen hukumarsa ya nuna.

Ya bayyana cewa, a wasu jihohin Arewa za a samu ruwa yadda aka saba samu, wasu kuma za su samu fiye da yadda suka saba, wasun kuma za a samu kasa ga yadda aka saba.

A Arewa ta Tsakiya za a samu ruwa fiye da yadda aka saba samu, hakazalika a wasu jihohi kamar Bauchi, Adamawa da Borno.

A bangare daya kuma jihohin Arewa maso Yamma irin su Arewacin Sakkwato, Zamfara, Katsina, Arewacin Kano, da Arewacin Jihar Jigawa, da Arewacin Jihar Neja za a samu karancin ruwa a kan yadda aka saba samu.

Tsawon daminar 2022

Ya ce tsawon daminar a yankin Kudancin Najeriya, za kai kwana 200 ana samu ruwan sama sosai.

A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa za a samu damina mai tsawon kwana 150 zuwa 200.

Yankin Arewa maso Gabas kuwa daminar ba za ta yi tsayi ba a wurare kamar kananan hukumomin Abadam, Gamboru-ngala, Gubio da ke Jihar Borno da ma sauran wuraren da ke Yankin Tafkin Chadi.

Haka abun zai kasance a wasu yankunan makwabciyarta, Jihar Yobe, wurare irin su Yusufari, Yunusare, Bade, Achida.

A Arewacin Jigawa, da Arewacin Katsina, da Arewacin Kebbi, da Sakkwato kuwa, tsawon daminar bana ba zai wuce kwana 70 zuwa 90 ba.