Ruwan saman bama-bamai!

Na san mai karatu ba zai taba mantawa da cewa mun tattauna matsalolin da suka shafi Boko Haram da ma duk wadansu abubuwa da suka shafi wannan batu a cikin wannan shafi, tsawon shekaru. Mun dai dauki tsawon watanni, muna neman sanin yaushe Boko ya zama Haram, wanda shi ne nazarin da nake jin ya […]

Ruwan saman bama-bamai!
Ruwan saman bama-bamai!

Na san mai karatu ba zai taba mantawa da cewa mun tattauna matsalolin da suka shafi Boko Haram da ma duk wadansu abubuwa da suka shafi wannan batu a cikin wannan shafi, tsawon shekaru. Mun dai dauki tsawon watanni, muna neman sanin yaushe Boko ya zama Haram, wanda shi ne nazarin da nake jin ya kokarta fayyace asali da dalilan abubuwan da suke ta faruwa tun daga shekarar 2009 zuwa yau.
Mun dai yi haka ne, ba don komai ba sai don kokarin saita tunanin mutane (shugabanni da masu bi) domin a sami kafar da ta dace wajen tunkarar wannan matsala da wata irinta, in ta taso. Mun yi haka ne ganin cewa ba abin da ya fi tarihi dadin lamari, domin a kullum taimakawa yake yi wajen gane kabli da ba’adi, da inda suka faru domin gyara.
Amma bisa ga dukkan alamu, batun sai kara lalacewa yake yi maimakon a samu mafita. A cikin ’yan kwanakin nan da suka wuce abubuwan da suka ko suke faruwa dangane da kashe-kashe da jefa bama-bamai a kasar nan ya kara sanya karayar zuciya ga yawancin mutane. Ba kuma wani abu ke kara jagula tunani ba irin ganin ba inda mafita ke bullowa kodai daga mahukuntan kasar ko kuma a tsakanin al’ummar da wannan ruwan bala’i ya auka mawa. Ba abin da mutane ke fatar gani irin a koma gidan jiya, gidan da kowa ke cikin walwala da jin dadi da gudanar da lamurra cikin kwanciyar hankali, koda kuwa ba a samu kawar da radadin talaucin da shi ma gyambo ne da ba a san makamarsa ba.
Idan dai a halin da muke ciki yanzu mutum ya ce ya fitar da rai ga samun saukin lamurra, musamman ganin karshen tashin-tashina da fashewar bama-bamai ko’ina da rasa rayuka ba ji, ba gani, ni ina ganin ba laifi ne ya yi ba. Kada kuma mai karatu ya yi mani fahimta ta baibai, amma alamun da ke tattare da mu cikin ’yan makonnin ba su nuna haske daga cikin duhu ba.
Me ya sa za mu ce haka? Idan mutum ya natsu da kyau ya yi nazarin irin labarai da sakonnin da ke ta watayawa a kafafen watsa labarai, ba abin da zai ci karo da shi sai yadda ake ta hadarin bama-bamai, a wasu wuraren kuma ruwan saman bama-baman ake ta faman yi. Abin ban haushi da tada hankali daga irin wadannan labarai ko sakonni shi ne wasu labarin kawai suke son ji. Ina aka jefa bam ko kuma wane wuri ne aka kai wa hari? Wasu kuma suna son sanin su wa suka mutu, ko su wa suka yi rauni daga harin bam kaza ko wani can daban? Wasu kuma ba abin da suka mayar da hankali irin yada jita-jita dangane da abubuwan da ke faruwa. Wasu kuma sai ka dauka murna ce a cikin ransu game da waki’ar da ta auka wa wasu, musamman idan yanki ko jihar da abin ya faru, nesa yake da nasu ko na ’yan uwa.
Irin wannan tunani ne ke sa mutane suke tambayar kansu wai shin ana kuwa neman mafita game da wannan lamari ko kuwa dai rawar dandali ce ake ta faman yi, ba kuma ranar fita daga fage?
Wani karin abin haushin shi ne ba inda za ka ga ana kokarta neman mafita daga wannan alkaba’i, sauran talakawa ba hus, ita gwamnati ta yi gum, sai in an kai sabon hari ka ji ana ta cece-ku-ce, tsohon hari da wadanda aka ce wai an kama, ana tuhuma, sun shiga kundin tarihi, ba a kara komawa kansu. Ba abin da aka iya, face dora laifi da zargi. Ai ba kowa ba ne ke wannan aika-aika sai gwamnati, ko kuma ai laifin na jam’iyya kaza ce ko kuma waccan. A wasu wuraren kuma, ana dora laifi ga yanki ko addini ko al’umma ko kuma wasu can daban, maganar neman mafita ba ta cikin lissafi.
Masana da masu ja gaba a fagen wayar da kai da ilimantar da al’umma da ake tsammanin su kasance tukunyar tafasa hanyoyin samar da mafita su kansu sun fada cikin tarkon ina-aka-saka-da-kashin-kare ko halin wuji-wuji-ina-gabas! A maimakon neman mafita da bin hanyar kawo karshen matsala ta kokarin neman su wane ne ke kai hari, me ya sa ko kuma su wa ke ba su kudin da suke sayen gaggan makamansu, an tsaya ana ta kallon kuda tsakanin masu goyon bayan harin bam a wani lokaci da masu suka da zagi ko kuma ’yan-ba-ruwanmu! Duka-duka dai mun kare cikin dimuwa da damuwa da rashin sanin makama da shiga cikin halin o-ni-’ya-su.
Shi ya sa a duk lokacin da na ji an ce ’yan ta’adda sun aiko da sako zuwa ga ’yan Najeriya, suna fadar sun yi nasara a hari kaza da kaza, ita kuma gwamnati na faman fadar muna nan muna kokarin kawo karshen ta’addanci sai na ce da kaina, su wane ne ’yan ta’addar na gaskiya? Me suke so? Shin hanyar kashe-kashe da fasa bama-bamai ita ce hanyar cimma kowace irin manufa? Shin lokaci bai yi ba da za a fito a yi ido hudu domin gane inda muka fito da inda za mu? Me zai hana a zauna bisa teburin sulhu da sasantawa, shin yin kemadagas da shan daga shi ne mafita? Shin akwai wani ciwo a doron kasa da bai da magani? Shin ’yan ta’adda ba mutane ba ne ko kuma ita hukuma ba ta san abin yi ba ne, har sai rayuka sun gama salwanta, sa’annan ne za a ce an sami magani?
Lokaci ya yi da al’ummar kasar nan ya kamata su kara hankalta domin kawo karshen wannan hargidiballe. Ta yaya? A gaya wa duk wanda ya kamata ya ji, ya ji, don ya tsawata da kuma wanda ya kamata ya sa a bari, a barin, idan ba haka ba kuwa, idan aka bari aka fara ba hammata iska ba alkali kusa ba mu san inda wannan zai kai mu ba!
Allah Ya sawwaka!