Ruwan teku ya koro wasikar da ta yi shekara 50 a cikin kwalba
An tsinci wasikar da wani mawallafi a yanzu dan kasar Birtaniya mai suna Paul Gilmore, ya saka a cikin kwalba shekara 50 da rubuta wasikar ya wurga a cikin teku. Paul, ya jefa wasikar ce lokacin da iyalansa suke komawa kasar Austireliya a 1960 wanda ba a tantance inda ya jefar ba a cikin tekun, […]
An tsinci wasikar da wani mawallafi a yanzu dan kasar Birtaniya mai suna Paul Gilmore, ya saka a cikin kwalba shekara 50 da rubuta wasikar ya wurga a cikin teku.
Paul, ya jefa wasikar ce lokacin da iyalansa suke komawa kasar Austireliya a 1960 wanda ba a tantance inda ya jefar ba a cikin tekun, kamar yadda ’yar uwar Paul ta sanar.
An tsinci kwalbar dauke da wasikar lokacin da ruwan tekun ya hankado ta gefen ruwa.
Paul Gilmore, ya jefa sakon nasa ne, a cikin ruwa tun yana shekara 13 a gefan wani jirgin ruwa da yake tafiya a cikin tekun ranar 17 ga Nuwamba 1969, lokacin shi da sauran ’yan uwansa suna yin hijira zuwa kasar Austireliya.
An gano wasikar ce a wannan mako, kuma dan Paul mai shekara 9 da ake kira Jyah, ya gano wannan wasikar a tekun Talia da ke Kudancin Austireliya.
Mahaifiyar Jyah, mai suna Carla Elliott, ta ce Paul ya yi mamakin ganin wannan takardar saboda a tunaninsa wasikar za ta iya zama ta bogi.
Misis Elliott, ta wallafa hoton wasikar a shafinta na sada zumunta Facebook, don a iya tabbatar da wasikar mallakin Mista Paul ce, kamar yadda kafar sadarwa ta Australian Broadcasting Corporation (ABC) ta sanar.
’Yar uwar Paul, Annie Crossland, da Mista Paul Gilmore, a yanzu haka suna tekun Baltic.