RUWASA za ta samar da ruwa ga yankunan Yobe
Hukumar Samar da Ruwan sha a Yankunan Karkara ta Jihar Yobe (RUWASA) da hadin gwiwar Bankin Raya kasashen Afirka (ADB) da Tarayyar Turai (EU) da Asusun Kula da Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF) sun kudiri niyyar samar da ruwa sha mai tsabta a sassan Jihar Yobe. Babban Manajan Hukumar RUWASA Kwamared Muhammad Bukar ne […]
Hukumar Samar da Ruwan sha a Yankunan Karkara ta Jihar Yobe (RUWASA) da hadin gwiwar Bankin Raya kasashen Afirka (ADB) da Tarayyar Turai (EU) da Asusun Kula da Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF) sun kudiri niyyar samar da ruwa sha mai tsabta a sassan Jihar Yobe. Babban Manajan Hukumar RUWASA Kwamared Muhammad Bukar ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da Aminiya a garin Damaturu. Kwamared Bukar ya ce hukumarsa da hadin gwiwar cibiyoyin za su yi duk abin da ya wajaba don samo hanyoyin samar da wadataccen ruwan sha mai tsabta a kananan hukumomin jihar 17. Ya roki gwamnatin jihar da ta sako wa hukumar wadatattun kudi don ta samu cika burinta na wadata al’ummomin jihar da ruwan sha kamar yadda manufar gwamnatin ta kunsa. Manajan ya nuna damuwarsa kan yadda jama’a ke gina wuraren tsuguno barkatai ba tare da la’akari da illar da hakan ke haifarwa ba, inda najasa ke gudana zuwa cikin rijiyoyin da ke samar da ruwan sha ga al’umma a karshe hakan kan haifar da yaduwar cutttukan da ke da alaka da shan gurbataccen ruwa. Ya nemi jama’a su kauce wa gina wuraren tsuguno a ko’ina da ina ba tare da neman shawarwari daga jami’an kiwon lafiya ba ko kuma wata hukumar da ke kula da hakan ba.