Rwanda ta haramta kiran Sallah da lasifika a masallatai
Hukumomin kasar Rwanda sun haramta wa dukan masallatan kasar amfani da lasifika domin kiran Sallah ko kuma gudanar da wani al’amari na addini. A yayin da take bayani game da sabuwar dokar, gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne saboda yadda kiran Sallar ke takura wa mutanen da ke makwabtaka da masallatan, kamar yadda ta […]

Hukumomin kasar Rwanda sun haramta wa dukan masallatan kasar amfani da lasifika domin kiran Sallah ko kuma gudanar da wani al’amari na addini.
A yayin da take bayani game da sabuwar dokar, gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne saboda yadda kiran Sallar ke takura wa mutanen da ke makwabtaka da masallatan, kamar yadda ta ce.
Sai dai kuma a nasu bangaren, al’ummar Musulmin Rwanda sun soki matakin gwamnatin. Sun bayyana cewa wannan matakin bai dace ba, musamman ganin cewa babu wani korafi da aka samu daga makwabtan masallatan da ke kasar, cewa ana takura musu. Don haka sun soki lamirin matakin hukumomin na haramta musu amfani da lasifika wajen gudanar da addininsu.
A cewarsa, maimakon a ce an hana amfani da lasifika gaba daya, kamata ya yi a ce a rika rage sauti a yayin kiran Sallah ko kuma gudanar da wa’azi da sauransu.
Sai dai ba wannan ne karon farko da hukumomin kasarRuwanda suke kafa dokoki ga masu addini ba, domin a kwanakin baya ma, gwamnatin ta rufe majami’u sama da 700, bisa dalilan tsaro da kuma abin da hukumomin suka kira da samar da kiwon lafiya ga al’ummar kasa.