Ryan Giggs ya zama Kocin Manchester United

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Manchester United da ke Ingila ya bayar da sanarwar korar Kocinsa Dabid Moyes kuma tuni ya maye gurbinsa da Ryan Giggs.Giggs yana daga cikin tsofaffin ’yan kwallon Manchester don haka kulob din ya yanke shawarar mayar da shi kocinsa kafin a kammala kakar wasa ta bana.Dabid […]

Ryan Giggs ya zama Kocin Manchester United
Ryan Giggs ya zama Kocin Manchester United

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Manchester United da ke Ingila ya bayar da sanarwar korar Kocinsa Dabid Moyes kuma tuni ya maye gurbinsa da Ryan Giggs.
Giggs yana daga cikin tsofaffin ’yan kwallon Manchester don haka kulob din ya yanke shawarar mayar da shi kocinsa kafin a kammala kakar wasa ta bana.
Dabid Moyes dan kimanin shekara 50 dan asalin Sukotlan ya karbi ragamar horar da ’yan kwallon kulob din ne a watan Yulin bara jim kadan bayan tsohon Koci Sa Aled Ferguson ya yi ritaya bayan ya shafe kimanin shekara 26 yana horar da kulob din.
Tun bayan da Moyes ya karbi ragamar kulob din al’amarurran wasa suka tabarbaew hasalima ya zuwa yanzu an doke kulob din a wasanni daban-daban har sau 11 a kakar wasa ta bana.
Abin da ya fi bakanwa wa magoya bayan kulob din rai shi ne yadda kulob din ya kasa hayewa gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da UEFA Champions League a kakar wasa mai zuwa.  Sannan babu wani kofi da kulob din ya lashe don haka za a iya cewa ya tashi a tutar babu a kakar wasa ta bana.