SA DA RAkUMI
SA DA RAkUMIWani Buzu da Bafulatani ne suka biya kudin tafiya Hajji, sai aka kira su zuwa filin jirgi. Bayan an fara kiran sunan Bafulatani ya ce “Sa.” Ashe Buzu ya ji haushi, da aka kira shi sai ya ce: “Rakumi.” Ya yi zaton wai kowa da sunan abin da yake kiwo zai amsa kiran. […]
SA DA RAkUMI
Wani Buzu da Bafulatani ne suka biya kudin tafiya Hajji, sai aka kira su zuwa filin jirgi. Bayan an fara kiran sunan Bafulatani ya ce “Sa.” Ashe Buzu ya ji haushi, da aka kira shi sai ya ce: “Rakumi.” Ya yi zaton wai kowa da sunan abin da yake kiwo zai amsa kiran.
Daga Baba Isah Ibrahim Idris, 08164643400
AZUMIN BANUFE
Wani Banufe ne lokacin azumi, yamma ta yi, ya kunna rediyo yana sauraro, kawai sai ya ji mutane suna buga waya, wannan ya ce a saka masa yabon Manzo (saw) tare da Fadar Bege; wani ya ce a saka masa tafsiri. Kawai Banufe da ya samu ya kira, aka dauka, aka ce waye? Sai ya ce: “Sunana Muhammadu Inda.” “To, Inda bismillah.” Inji mai gabatarwa. Shi kuwa kawai sai ya ce: A saka mini Kiran Sallah, domin muna so mu sha ruwa ne saboda azumi!”
Daga Garba Sabiyola Gashuwa, 08096284154
BASAKKWACE
Wani Basakkwace ne da azumi yana narkar abinci da Asuba sai wani abokin zamansa ya ce: “Kai dan Sakkwato, an kira Assalatu!” Sai ya ce: “Asalatu ehona, sai na ji warabbana.”
SAURAYI DA BUDURWA
Wata hadaddiyar budurwa ce ta tsaya a kofar gida, sai ga wani saurayi ya zo wucewa, sai ya tsaya tun daga nesa yana kallon ta. Ya lura da cewa ashe ita ma kallon shi take yi, kawai sai ya canja tafiya, ya nufi wajenta. Yana isa gare ta sai ya ce mata: “Sannu kyakkyawa, daman na zo zan wuce ne sai na ga kina kallona, don haka tun da mun aminta da juna ya za a yi ke nan?” Sai budurwar nan ta fashe da dariya ta ce: “Ba wani abu ba ne ya sa nake kallon ka ba, wallahi ka yi mini kama da wani biri da ya tsinke ya gudu daga gun mai shi ne dazu a kasuwa.
Daga Umar Adamu Isah, 08064385252