Sa ido a zabe: ’Yan siyasar Zimbabwe sun ki amincewa da Obasanjo

kungiyar Pan African Forum ta ki amincewa da shawarar da Tarayyar Afirka (AU) ta yanke na nada tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo a matsayin shugaban kungiyar sanya ido na AU a zaben da za a gudanar a kasar Zimbabwe a ranar 31 ga Yuli mai zuwa. Shugaban kungiyar Dabid Nyekorach-Matsanga ya ce, tsohon Shugaban na […]

Sa ido a zabe: ’Yan siyasar Zimbabwe sun ki amincewa da Obasanjo

Cif Olusegun Obasanjokungiyar Pan African Forum ta ki amincewa da shawarar da Tarayyar Afirka (AU) ta yanke na nada tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo a matsayin shugaban kungiyar sanya ido na AU a zaben da za a gudanar a kasar Zimbabwe a ranar 31 ga Yuli mai zuwa. Shugaban kungiyar Dabid Nyekorach-Matsanga ya ce, tsohon Shugaban na Najeriya yana da matukar akidar raba kan jama’a ta yadda zai iya jawo matsala irin ta kasar Masar a Zimbabwe. kungiyar ta kuma bayyana Obasanjo a matsayin munafuki wanda ya ci amanar Afirka a lokutan sanya ido kan zabubbukan baya a sassan yankin.
Nyekorach-Matsanga ya ce, Obasanjo ya tsani Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe, kuma “yana goyon bayan ’yan adawa,” lamarin da ya ce, na iya jawo rikici a zaben. Ya ce, Obasanjo ya jawo matsala lokacin da ya jagoranci sa ido a zaben kasar Togo da Senegal, kuma lokacin da ya shiga tsakani a rikicin Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo  ya jawo matsala.
Shugaban ya ce, Obasanjo ba shi da wata shaida ta dimokuradiyya da zai iya sanya ido kan zabe, domin a kasarsa Najeriya ya yi yunkurin canja tsarin mulki don yin ta-zarce a shekarar 2006 don yin mulki karo na uku. Kuma ya ce Obasanjo ba zai iya zama dan ba-ruwanmu a zaben ba, saboda ya taba kiran a kawar da Mugabe daga mulki koda ta tashin hankali, kuma ya nuna goyon baya ga Morgan Tsbangarai. Ya ce su ba magoya bayan Mugabe ba ne, su masu kaunar kasar ce da ba su son kasar ta wargaje.