Sa Ubangiji da farko (1)

“Muhimmin abu na farko, sai ku kwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah da kuma adalcinSa, har ma za a kara muku dukkan wadannan abubuwa.” Matiyu 6:33. Godiya ta tabbata ga Ubangiji Allah Mai iko duka domin wannan kyakkyawan zarafi da Ya ba mu don mu yi nazari a kan maganarSa. Makonin da suka shige mun […]

Sa Ubangiji da farko (1)

“Muhimmin abu na farko, sai ku kwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah da kuma adalcinSa, har ma za a kara muku dukkan wadannan abubuwa.” Matiyu 6:33.

Godiya ta tabbata ga Ubangiji Allah Mai iko duka domin wannan kyakkyawan zarafi da Ya ba mu don mu yi nazari a kan maganarSa.

Makonin da suka shige mun yi bincike a kan Ubangiji ne Madogararmu, a wannan makon za mu ga me ya cancanta ya fi zama mafi muhimmanci cikin rayuwarmu; wato abu na farko cikin rayuwar mai bin Yesu Almasihu.

Kamar yadda muka karanta cikin karatunmu na farko cewa muhimmin abu na farko da ya kamata dan Adam ya kwallafa ransa bisa kuwa shi ne Mulkin Ubangiji Allah, wato abubuwan da suka shafi Ubangiji.

Muna cikin rayuwa ce da za ka ga a kowace rana muna cikin kaiwa-da-kawowa, zuwa ofis, makaranta, masana’antu, kasuwa da makamantansu. Yana da kyau kwarai da gaske mu zama marasa kyuya, amma, a cikin ayyukanmu na yau da kullum, muna bidar nufin Ubangiji da farko kuwa? Idan fa madogararmu Ubangiji ne, babu shakka abin da ya kamata mu bida da farko shi ne nufin Ubangiji cikin komai a koyaushe. Babu shakka idan muka sa Ubangiji da farko cikin kowane al’amarinmu za mu ga albarkar Ubangiji mara iyaka kuma kowane abin da muka sa a gabanmu za mu ci nasara. Sau da dama a wasu lokuta, cikin saninmu ko rashin sani, mukan bar wasu harkokinmu su dauke gurbin Ubangiji cikin rayuwarmu. Abin nufi a nan shi ne mukan dauki ayyukan da muke yi su zama mana tushen rayuwa, mukan sa karfinmu da iliminmu da dukiyarmu duk a ciki, mu kuma bi namu tafarkin ganin cewa idan har ba mu sa karfinmu ko lokacinmu ciki ba, ba za mu samu nasara ba. Mukan manta cewa nasara daga wurin Ubangiji ne kadai, kada mu bauta wa ayyukanmu ko kasuwancinmu, sai dai Ubangiji Allah kadai. Wadansu suna ganin cewa ai bautar gumaka sai ka sassaka wata siffar dabba ko ka gina wata halitta kana bautawa shi ne ake nufi da bautar gumaka, ba a nan kadai ta tsaya ba, duk abin da ka dauka ka so fiye da Ubangiji Allah bautar gumaka ce. Saboda haka a zamanka na mai bin Yesu Almasihu, sai ka mai da hankali ka natsu ka bi gurbin da ya bar mana kamar yadda shi ya yi lokacin da yake cikin duniya. Idan muka duba cikin Littafin Kolosiyawa 3:1-4, “To, da yake an tashe ku tare da Almasihu, sai ku nemi abubuwan da suke a Sama, inda Almasihu yake, a zaune a dama ga Allah. Ku ƙwallafa ranku a kan abubuwan da suke Sama, ba a kan abubuwan da suke a ƙasa ba. Gama kun mutu, ranku kuwa a ɓoye yake a gun Almasihu cikin Allah. Sa’ar da Almasihu wanda yake shi ne ranmu ya bayyana, sai kuma ku bayyana tare da shi a cikin ɗaukaka.” To, da sanin wannan fa sai mu roki Ubangiji Ya jagorance mu cikin aikace-aikacenmu da harkokinmu na yau da kullum kamar yadda Littafi Mai tsarki ya fada, “Ka roki Ubangiji, Ya sa albarka ga shirye-shiryenka, za ka kuwa yi nasara cikin aikata su.”  Karin magana 16:3.

Mu bar halinmu na mutuntaka mu nemi nufin Ubanmu da ke cikin sama, wanda ya cika mu da RuhunSa mai tsarki don irin wannan lokaci.

Sai mu bar abuta da duniya da kuma abin da ke cikinta, don abota da duniya kan sa mutum ya bar sa Ubangiji Allah da farko cikin rayuwarsa, sha’awace-sha’awacen kayan duniya baza su taba bari mu nemi fuskar Ubangiji ba. Saboda haka, wajibi ne mu nemi nufin Ubangiji Allah cikin komai a rayuwan nan. Littafin Yakubu 4:4-8 na cewa; “Maciya amana! Ashe, ba ku sani abota da duniya gaba ce da Allah ba? Saboda haka, duk mai son abota da duniya, ya mai da kansa mai gaba da Allah ke nan. Ko kuna tsammani a banza ne nassi ya ce, “Wannan ruhu da Allah Ya sa a cikinmu yana tsaronmu kwarai?” Allah Shi Yake yin mayalwacin alheri. Domin haka nassi ya ce, “Allah Yana gaba da masu girman kai, amma Yana yi wa masu tawali’u alheri.” Saboda haka, ku mika kanku ga Allah, ku yi tsayayya da Iblis, lallai kuwa zai guje muku. Ku kusanci Allah, Shi ma zai kusance ku. Ku tsarkake al’amuranku, ya ku masu zunubi! Ku kuma tsarkake zukatanku, ya ku masu zuciya biyu!”

“Masu zaman halin mutuntaka, ai, kwallafa ransu ga al’amuran halin mutuntaka suke yi, masu zaman ruhu kuwa ga al’amuran ruhu.”  Romawa 8:5

Bari Ubangiji Allah Ya jagorance mu, amin.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos