Sa’adatu Ali JC ta raba wa mata 150 injinan markaɗe a Gombe
Ta ce tallafin wani ɓangare ne na rage talauci a tsakanin al’ummar yankin.

A yayin bikin Ranar Mata ta Duniya, Hajiya Sa’adatu Ali Isa JC, matar Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Balanga da Billiri, ta tallafa wa mata 150 da injinan markaɗe domin su samu hanyar dogaro da kai.
Da ta ke jawabi yayin rabon kayan, Hajiya Sa’adatu ta ce manufar wannan tallafi ita ce taimaka wa mata su samu sana’a da za ta rage musu dogaro da wasu.
- PDP ta sake ɗage babban taronta zuwa Mayun 2025
- An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba
“Wannan tallafi yana da muhimmanci domin zai taimaka wa mata su kula da kansu da iyalansu ba tare da jira komai daga mazajensu ba.
“Wannan kuma wani yunƙuri ne na taimakon jama’a kamar yadda maigidana, Hon. Ali Isa JC, ke yi a kodayaushe,” in ji ta.
Ta bayyana cewa mijinta ya tallafa wa mutum sama da 2,000 da kayan abinci da na noman rani don rage yunwa a cikin al’umma.
Haka kuma, ta taɓa koyawa wasu mata sana’ar yin takalma, wanda har takalmansu ke zuwa ƙasashen waje saboda ingancinsu.
Hajiya Sa’adatu ta ja hankalin matan da suka amfana da injinan da ka da su sayar da su, sai dai su yi amfani da su don amfanin kansu da iyalansu.
“Idan kuka yi amfani da wannan tallafi yadda ya kamata, zai zamo muku wata babbar hanya ta samun riba kamar yadda waɗanda suka koyi sana’ar takalma suka samu nasara,” inji ta.
Sannan ta yi kira ga masu hali da su taimaka wa jama’a, ba sai ‘yan siyasa kaɗai ba, domin hakan zai rage zaman banza da talauci a cikin al’umma.
Wasu daga cikin matan da suka amfana sun jinjina mata, inda suka ce ta zama abin koyi a cikin mata.