Sababbin jihohi ne ko dawo da ma’aikatar ma’adinai?
Wani kwamitin babban taron kasa a Abuja ya bayar da shawarar kirkiro karin wasu jihohi 18. Idan har gwamnatin tarayya ta amince da wannan shawarar, ta kuma aike wa Majalisar kasa don neman yardarta game da haka, yawan jihohin kasar nan za su zama 54 ke nan. Bisa ga shawarwarin da kwamitin babban taron ya […]
Wani kwamitin babban taron kasa a Abuja ya bayar da shawarar kirkiro karin wasu jihohi 18. Idan har gwamnatin tarayya ta amince da wannan shawarar, ta kuma aike wa Majalisar kasa don neman yardarta game da haka, yawan jihohin kasar nan za su zama 54 ke nan. Bisa ga shawarwarin da kwamitin babban taron ya bayar za a yi karin jihohi uku-uku a kowace shiyya don su zama tara-tara, kuma hakan zai hada ne da karin wata guda a shiyyar Kudu-maso-Gabas wacce ke da jihohi biyar ba kaman sauran da ke da shida-shida ba.
Kwamitin ya rattaba sunayen guda 16 daga cikin jihohin da yake so a kirkiro, kuma sai nan gaba ne zai fayyace sunayen sauran guda biyun da za a kirkira a shiyyoyin Kudu-Kudu da Kudu-maso-Yamma da kuma garuruwan da hedkwatocinsu za su kasance. Taron ya ce duk wata sabuwar jihar da za a kirkiro wajibi ne ta kasance za ta iya zama dirshan da gindinta, ba wai ta jingina kan wata ‘yaruwarta ko gwamnatin tarayya ba.
To amma sai dai tun kafin a tafi ko’ina game da wannan batun sai ga shi nan jama’a na ta sukar lamirin babban taron dangane da haka. Wasunsu na cewa ai an yi ne ba a yi ba, domin sau da yawa babban taron ya sha yin kudurori game da bukatar rage yawan kudin da ake batarwa wajen gudanar da harkokin mulkin kasar nan, sai kuma ga shi nan taron ya yi amai, ya kuma lashe, ya dauki matakin da ya saba wadancan kudurorin, domin kuwa karin jihohi zai kara janyo matsalolin da suka nunka wadanda ake fama da su a halin yanzu game da batun kudin sarrafa su.
Baicin haka nan kuma mutane da yawa na da’awar cewa kirkiro karin jihohi a halin yanzu ganganci ne babba, musamman ma ganin yadda wasu jihohin ba su iya rike kansu, sun dogara ne kacokan daga dan dillen da suke samu daga gwamnatin tarayya.
Irin wadannan jihohin ba su iya tabuka komai bayan sun biya albashin ma’aikata, sai kawai su nannade hannu su jira wani jikon. Kai hatta ma kudin shiga daga cikin albarkatun da Buwayi ya huwace musu ba su iya tarawa, saboda sakaci ko ragwanci ko rashawar da ta yi musu katutu. Shi ya sa wasu mutane ke jin cewa zai fi kyau a dunkule wasu jihohin don su zama guda daya, kwakkwara, wacce za ta iya biyan dukkan bukatunta ba tare da shiga matsalolin da ke hana jihohi kumari da armashi ba. To amma babban taron ya ki amincewa da wata shawarar da kwamitin ya bayar na cewa ya kamata a yi haka domin a ganinsa karin jihohin shi ne abin da jama’a ke so, kuma mafi a’ala ga ci gaban kasa.
A bisa gaskiya batun karin jihohi al’amari ne mai fuskoki biyu, kuma kowacce na da nata fa’idar da kuma illa. Amma idan aka yi la’akari da irin hujjojin da masu neman sababbin jihohi ke gabatarwa, musamman ma na neman kawo karshen zaman doya da manjan da ake yi tsakanin kabilun wasu jihohin da kuma kwadayin habakar tattalin arziki cikin hanzari sai a fahimci wajibcin yin haka. Haka nan kuma idan aka lura da yadda gwamnatocin jihohi da kananan hukumominsu ke zaman hannu-baka-hannu-kwarya, suna yawan bulaguro zuwa Abuja da kokunan bara a hannayensu sai a tabbatar wadannan sun zama kaya, ba su iya tabuka komai balle jama’arsu su ci gajiyarsu.
To amma duk me ya janyo haka? Rashin farfado da aikin gona gadan-gadan da kuma kakkafa kananan masana’antu a kauyuka don sarrafa amfanin gonar kafin a kai shi manyan masana’antu a birane don samar da kayayyakin da za su wadata a cikin gida, a kuma fitar da rarar don sayarwa a wasu kasashe.
Ai sanin kowa ne cewa jihohin Arewa na zaune ne bisa dimbin arzikin ma’adinai, kuma albarkar da ke karkashin wata jiha guda daya ta fi rabin arzikin man fetur din da wasu jihohin kudu ke yi masu dodorido da shi.
To amma me ke hana cin gajiyar wadannan albarkatu da ma’adinan? Dokar kundin tsarin muki da ta mallaka dukkan arzikin da ke jibge a karkashin kasar nan a hannun gwamnatin tarayya ce, kuma har yanzu ba ta kammala tsara manufar da za ta bayar da dama ga jihohin da ke da arzikin su fara cin moriyarsu ba. Soke ma’aikatar ma’adinai (solid minerals) ya kara hana jihohi cin arzikin albarkatun da suke da shi. Tilas ne a dage wajen ganin an dawo da wannan ma’aikata don jihohin Arewa su dinga cin gajiyar wannan arziki, su huta da gorin da ake yi masu akan man fetur.
Da gangar an kawar da hankulan jama’a game da arzikin da ke jibge a karkashin kasa a Arewa ana ta hauragiya kan man fetur, kamar shi kadai ne albarkar da Allah Ya hore wa kasar. Irin abin da ya kamata ke nan a ce babban taron ya mayar da hankalinsa akai, watau tsara hanyoyi da dabarun da jihohin kasar nan za su bi don kaiwa ga tono dimbin albarkatun da suke kwankwace akai, maimakon tsayawa suna ta cacar baki kan kirkiro sababbin jihohi samun mukaman gwamnoni da na sanatoci da ministoci da kwamishinoni.