Sababbin ’yan kungiyar Ombatse suna kai hare-hare a kauyukan Nasarawa

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta umarci hukumomin tsaro a jihar su soma gudanar da bincike cikin gaggawa don kamo tare da hukunta ’ya’yan sabuwar kungiyar Ombatse da suke kai hare-hare a wasu kauyukan jihar. Shugaban Majalisar Honorabul Balarabe Abdullahi Muhammed ne ya ba da umurnin bayan zaman gaggawa da ’yan majalisar suka yi a ranar […]

Sababbin ’yan kungiyar Ombatse suna kai hare-hare a kauyukan Nasarawa
Sababbin ’yan kungiyar Ombatse suna kai hare-hare a kauyukan Nasarawa

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta umarci hukumomin tsaro a jihar su soma gudanar da bincike cikin gaggawa don kamo tare da hukunta ’ya’yan sabuwar kungiyar Ombatse da suke kai hare-hare a wasu kauyukan jihar.
Shugaban Majalisar Honorabul Balarabe Abdullahi Muhammed ne ya ba da umurnin bayan zaman gaggawa da ’yan majalisar suka yi a ranar Litinin da ta gabata a Lafiya.
Shugaban ya ce ya zame wa majalisar dole ta ba da umarnin saboda la’akari da yadda ’ya’yan sabuwar kungiyar ta Ombatse ke ci gaba da kai hare-hare a wasu kauyukan jihar inda suke kashe mutane suna ikirarin cewa su sababbin ’yan kungiyar Ombatse ne.
 Tun farko a lokacin zaman majalisar wakilin Nasarawa-Eggon ta Arewa Honorabul Aga Muluku ya ce bayan gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro sun dakile ayyukan ’ya’yan kungiyar inda suka rusa ta kwata-kwata wadansu sun fito yanzu suna cewa su ’ya’yan sabuwar kungiyar ce. A cewarsa al’ummar Eggon a jihar mutane ne masu son zaman lafiya inda ya musanta jita-jitar da wadansu ke yadawa cewa sabuwar kungiyar Ombatse din ta ’yan kabilar Eggon ne.
Idan ba a manta ba, ’yan kungiyar Ombatse sun taba kai hari a kauyen Alakyo da ke karamar Hukumar Lafiya inda suka kashe sama da jami’an tsaro 100 kafin gwamnatin jihar da jami’an tsaro su  shawo kansu daga baya suka rusa kungiyar.