Sababbin ’yan wasa mata da ke tashe a Amurka
Harkar fim a duniya ta dade tana daukar hankalin mutane, musamman kuma idan ana batun inda harkar ta bunkasa, kasar Amurka na kan gaba. A ’yan shekarun nan, an samu matasa kuma sabbin mata ’yan fim da suke tashe kuma ake yayinsu.Wadanne ’yan wasa ne ke kan gaba a tashe? Bincken Aminiya ya gano zaratan […]

Harkar fim a duniya ta dade tana daukar hankalin mutane, musamman kuma idan ana batun inda harkar ta bunkasa, kasar Amurka na kan gaba. A ’yan shekarun nan, an samu matasa kuma sabbin mata ’yan fim da suke tashe kuma ake yayinsu.
Wadanne ’yan wasa ne ke kan gaba a tashe? Bincken Aminiya ya gano zaratan ’yan wasa guda hudu da ake yayi. Wadannan kuwa sun hada da Chloe Grace Moretz da Hailee Steinfeld da Lily Collins da kuma Ashley Madekwe.
Chloe Grace Moretz ta bunkasa martabarta a harkar fim a sanadiyyar kokarinta a fina-finan ‘Carrie’ da kuma ‘Kick Ass 2.’ ’Yan kallo suna kaunarta, a yayin da sunanta ya karade ko’ina. Ta bangaren sutura kuwa, ’yar wasan ta fi mu’amala da suturun kamfanonin Dolce & Gabbana, balentino da kuma na Chanel.
Ita kuwa Hailee Steinfeld ta shahara ne da fina-finanta da suka dauki hankalin mutane, wato fina-finan ‘Romeo & Juliet’ da ‘Ender’s Game.’ Ita ce matashiyar ’yar wasa mafi karancin shekaru da aka taba zaba domin cin kyautar ‘Academy Award.’
Lily Collins, ’yar wasa ce da ita ma tauraruwarta ke haskawa, musamman yadda ta kware wajen taka rawa a fina-finai da ma dukkan aikin da ta dora hannu a cikinsa.
Sai kuma Ashley Madekwe, wacce ta dauki hankalin mutane a fim din ‘Hamptons on Rebenge.’ Ta kware sosai wajen tallata suturun zamani.



