Sababbin yankan rake a siyasa suka nakasa kasar nan – Hassan Yusuf
Fitaccen dan siyasar nan kuma halifan marigayyi Malama Aminu Kano Alhaji Hassan Yusuf ya ce sababbin yankan rake da suka mamaye harkokin siyasar kasar nan ne suka kawo nakasu ga Arewa da ita kanta kasar kasancewar ba su da hangen nesar da za su iya kai al’umma ga gaci.Halifa Hassan Yusuf wanda ya tsaya takarar […]

Fitaccen dan siyasar nan kuma halifan marigayyi Malama Aminu Kano Alhaji Hassan Yusuf ya ce sababbin yankan rake da suka mamaye harkokin siyasar kasar nan ne suka kawo nakasu ga Arewa da ita kanta kasar kasancewar ba su da hangen nesar da za su iya kai al’umma ga gaci.
Halifa Hassan Yusuf wanda ya tsaya takarar Shugaban kasa a rusasshiyar Jam’iyyar PRP a Jamhuriya ta Biyu ya shaida wa Aminiya haka ne a garin a Damaturu game da rashin zaman lafiya a Arewa da kuma tabarbarewar tattalin arziki.
Alhaji Hassan Yusuf ya ce, wannan lamari na mayar da matasa su jagoranci harkokin siyasar kasar nan ya samo asali ne lokacin da shugaban mulkin soja Janar Ibrahim Babangida ya nuna kiyayyarsa ga jagorancin tsofaffin jini a harkokin siyasa ya maye gurbin su da sababbin jini, “To tun wancan lokacin harkokin siyasar kasar nan suka fara samun koma baya musamman a Arewa da ita ce jagora kan abin da ya shafi shimfida mulki irin na dimokuradiyya.
Ya ce ba wai yana cewa matasan ba su cancanci jagorancin kasar da al’umma ba ne, abin nufi shi ne yadda aka bar su su kadai ba tare da gwamutsa su da dattawa masu hangen nesa ba, domin in sun kauce hanya su nusar da su. “Wannan shi ne babbar illar da ta jefa Arewa da kasa kacokan cikin halin rashin tabbas da ake ciki,’ inji shi.
Halifa Hassan ya ce duk wanda ya san kasar nan a lokacin Jamhuriya ta Biyu lokacin da dattawa ke jan akalar siyasar al’umma ya san akwai bambanci mai yawa da yanzu.
Ya kara da cewar akwai lokacin da ya halarci wani taron siyasa gab da zai bar siyasa inda ya ba da wata shawara muhimmiya amma nan take wani yaro ya tashi tsaye ya mayar masa martani cewa, wai abin da ya fada tsohon yayi ne, yanzu suna cikin sabon salon siyasa ne.
A cewarsa wannan abu da matshin dan siyasar ya fada masa ya ba shi mamaki da al’ajabi kuma tun lokacin ya san siyasar kasar nan ta shiga rudu.
Don haka ya kirayi matasa ’yan siyasa na yankin Arewa su yi karatun ta-natsu wajen kokarin ceto yankin daga halin rashin tabbas da yak e ciki, in ba haka ba yara ma su zuwa ba za su yafe musu ba.
Sai ya kalubalanci masu kiran kansu da Dattawan Arewa su hanzarta ceto yankin daga halin da yake ciki tun kafin al’amura su gama tabarbarewa.