Sabanin shugabanni

Ya zama dabi’a a siyasar Najeriya da zarar an yi sabon zabe sai tsofaffin  ’yan siyasa su shiga gaba da sababbin mahukuntna! Shugabanci kan zama kamar tsarin tasiri a kan wadansu mutane, ta yadda shugaban zai rinjaye ra’ayoyin wadanda yake mulka. Duk abin da muka yi a kan nuna irin shugabancin da yake tafiyar da […]

Sabanin shugabanni

Ya zama dabi’a a siyasar Najeriya da zarar an yi sabon zabe sai tsofaffin  ’yan siyasa su shiga gaba da sababbin mahukuntna! Shugabanci kan zama kamar tsarin tasiri a kan wadansu mutane, ta yadda shugaban zai rinjaye ra’ayoyin wadanda yake mulka.

Duk abin da muka yi a kan nuna irin shugabancin da yake tafiyar da mu, kamar yadda akan yi halin ko-in-kula, haka yadda muke sa kayan sawa, yadda muke magana, duk tsarin kan koma kan shugaban ne.  Misali lokacin da Shugaba Buhari ya hau mulki da zimmar yakar cin hanci da rashawa kowa ya shiga taitayinsa! Daga bisani sai aka gane Buharin ba na da ba ne, wato lokacin da ya yi mulkin soja, sai aka shiga turka-turka da direban!

Akwai illoli da dama da sabanin shugabanni ke haifarwa musamman ga rayuwar matasa. Farawa da rashin ganin girman na gaba, inda yara kan raina iyayensu da yayyensu, da malamansu.

Yau a Kano an raba gari tsakanin Kwankwasiyya da Gandujiyya, kowa na shirin ganin bayan dan uwansa.  Abin takaicin shi ne duk wanda ya yi fushi da fushin wani zai fuskanci fushin Ubangiji.

Sabani a Kaduna ko Kano, ba a jihohin ya tsaya ba, fitinar ta shafi Arewa, kuma tana neman shanye kasar, musmaman jami’yya mai mulki, ganin an kashe adawa a jihohi irin su Katsina za a koma adawar cikin gida, inda jam’iyya kan dare gida biyu ko gidaje masu akidu mabambanta!

Yayin da a Jihar Katsina Gwamnan ya gina gadar kasa, ta yadda ya mayar da jihar ta jam’iyya daya! Wadansu masana na ganin ya yi haka ne don a sayar masa da tiketin shi kadai a burinsa na zarcewa a karo na biyu. 

 Sai dai wadansu masana siyasa na ganin gadar na iya ruftawa domin akwai yiwuwar a sauya wakilai (masu zabe, wato deleget) daga hedkwatar jam’iyya don shara, sannan akwai wadansu ’yan cikin gida masu uwa a gindin murhu da suke da burin su ma sai an jera su a gwamnonin Jihar Katsina.

Duk da cewa Shugaban kasa bai bayyana zai tsaya takara ba ko zai koma gidan gonarsa a Daura, amma gwamnoni da dama sun yi masa alkawarin ba shi kuri’u, wadansu ma sun yi alkawarin kawo fiye da wadanda suka zabe shi a farko ba tare da la’akari da ra’ayin talakawa ba. 

Amma a wasu jihohi an yi zargin har yara da awaki ake karawa a cikin masu rajistar zabe inda duk da karancin fitowa a kada kuri’u don halin da aka shiga na bazatar sauyi!

A wasu jihohi kamar Kaduna abokan adawa sun yi wa Gwamnan yawa duk da haka ana ganin sai an yi amfani da karfin jam’iyya don ganin Gwamnan ya koma kan kujerarsa. 

Abokan adawan sun wuce  daidaikun mutane har da kungiyoyi irin su kungiyar Malamai ta kasa (NUT) da kungiyar Ma’aikatan kananan Hukumomi (NULGE) da kungiyar kwadago (NLC) da ta ’yan kasuwa da ta dalibai da sauransu. 

Matsayar da gwamnoni da sanatoci ke dauka na da illa ga mabiya da ’ya’yan jam’iyya da kasa, maimakon a ga misalin tafiyarwa a gari irin Kano.

Maganar gaskiya Ganduje ya fi gaskiya ta fuskar shi yake mulki. A lokacin da Kwankwaso ya yi zamaninsa wa ya sa masa baki? Kuma da aka ce kowane Gwamna shi ne shugaban jami’yya a jiharsa Shekarau yana ji yana gani ya hakura, me ya sa Kwankwaso ba zai bi sahu ba?

To, idan Kwankwaso ya ki bin shawara, don burge mabiya, ya ki kama bakinsa, wadannan mabiyan za su kai shi su baro a can. Domin za a kirga shi a cikin wadanda suka janyo fitina bayan sun kawo alheri! Yaushe zai kawo wani alherin da zai rufe wannan bala’in da aka kunno a Kano?

Ko yau ka je Kano sai ka iske gungun matasa suna zaune ba sa zuwa makaranta, ba su da sana’a, amma jira suke ya zo su yi masa caffa! 

 Ita kanta Hukumar Zabe ta kasa tana fuskantar barazanar rashin tsaron ma’aikanta da aringizon kuri’u kamar yadda ake zargin har dabbobi aka yi amfani da su wajen kada kuri’a a wasu lokuta a baya.

Don haka akwai bukatar shugabanni su yi karatun ta-natsu don ganin abubuwa sun daidaita a kasar nan.

Allah Ya tsare mu.

 

Buhari Daure

[email protected]

Modoji, Katsina.