Sabbin abubuwan da ke faruwa a yakin Rasha da Ukraine
Netflix, TikTok, Master Card da Visa sun rufe harkokinsu a Rasha; Gwamnati ta kayyade sayen kayan abinci
Ma’aikatar tsaro ta Ukraine ta ce mayakan sa-kai 20,000 daga kasashen duniya za su taimaka wa kasar wajen yakar Rasha; Amma Shugaban Rasha, Vladimir Puti, ya ce kasarsa ce da nasara, ko ta sulhu, ko ta yaki.
A yayin da kasashen ke ci gaba da gwabza fada a tsakaninsu, kafar sada zumunta ta TikTok da kuma Netflix mai yada fina-finai ta intanet sun dakatar da harkokinsu a Rasha.
- Rasha ta harba wa Ukraine makamai masu linzami 600
- NAJERIYA A YAU: Sirrin Da Bello Turji Ya Bayyana Mana A Maboyarsa
Su ma manyan kamfanonin katin cirar kudi na Master Card, Visa da sauransu sun rufe harkokinsu a Rasha, inda gwamnatin kasar ta kayyade sayen kayan abinci a halin yanzu.
Ga jerin sabbin abubuwan da suka faru:
– Ruwan bama-bamai –
Sojojin Rasha sun tsananta luguden bama-bamai yi a sassan kasar Ukraine inda Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum akalla miliyan 1.5 sun tsere a cikin kwana 10 da aka fara yakin.
Ta ce rabon da mutane masu wannan yawa su fice da wata kasa a cikin kwana 10 tun a lokacin Yakin Duniya II.
– Fararen hula sun makale a Mariupol –
Yunkurin kwashe fararen hula daga birnin Mariupol ya sake gagara kan zargin saba yarjejeniyar tsagaita wuta.
Mazauna birnin suna fama da rashin ruwan sha da wutar lantarki; Amma ma’aikatar tsaron Rasha ta ce za ta bari a gudanar da ayyukan jinkai a wasu sassan Ukraine.
– Musayar wuta –
Sojojin Ukaine sun ce an ci gaba da kazamin fada tsakaninsu da dakarun Rasha a kusa da birnin Mykilayiv da ke Kudancin kasar.
Birnin Mykilayiv na kan hanyar zuwa babbar tashar jiragen ruwan Ukraine da ke Odessa.
– An ragargaza Chernihiv –
An kashe fararen hula da dama a Chernihiv da ke Arewacin Ukarine.
Wadanda ke da ransu kuma sun koma zama a cikin baraguzan gini da kangaye.
– An lalata filin jirgi –
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya yi zargin cewa makamai masu linzami da Rasha ta harba sun lalata filin jirgin Vinnytsia da ke tsakiyar kasarsa.
– Rasha ta kayyade sayen kayan abinci –
Rasha ta kayyade wa masu kantuna sayar da muhimman kayan abinci a yunkurinta na yakar labarin da ke cewa takunkumin da Kasashen Yamma suka kakaba mata za ta kara muni.
– An tsare dubban masu zanga-zanga –
Jami’an tsaron Rasha sun tsare wasu dubbun mutane da suka fito zanga-zangar kyamar yakar Ukrain da kasar ke yi.
Daga fara yankin zuwa yanzu, mutanen da aka tsare kan gudanar da zanga-zanga sun haurwa 11,000.
– Duk yadda ta juya mu ne a sama —Putin –
Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin, ya ce kasarsa za ta cim ma manufar da ta sa gaba a Ukraine, “ko ta sulhu ko ta yaki”.
– Poland za ta ba Ukriane jiragen yaki –
Amurka ta amince kasar Poland ta tura wa Ukraine jiragen yaki, abin da Putin ya yi gargadi cewa na iya tsoma kasashen kungiyar tsaro ta NATO a yakin da babu ruwansu.
– Takunkumin danyen mai –
Sakataren Amurka, Antony Blinken ya ce Kasashen Yamma na duba yiwuwar kaurace wa danyen man da Rasha ke samarwa.
Sai dai ko a yanzu farashin gangar danyen mai samfurin Brent na Amurka ya doshi Dala $140, wanda shi ne mafi tsada.
– Rufe katin cirar kudi –
Manyan kamfanonin cirar kudi na Visa, Mastercard da kuma American Express sun rufe harkokinsu a Rasha.
Amma bankunan Rasha sun ce za su koma amfani da UnionPay na kasar China.
– Ficewar kwararru –
Manyan kamfanonin kwararru na KPMG da PwC sun rufe harkokinsu a Rasha, wanda ke nufin mutum 8,200 za su rasa ayyukansu.
Shi ma kamfanin kwararru na Deloitte na nazari kan yiwuwar zama ko ficewa daga kasar.
– Fargabar nukiliya –
Faransa ta ce za ta tura wa Ukraine kwayoyin magani na iodine da sauran magunguna domin kare mutane daga illar tuturin nukiliya.
– Mayakan sa-kai –
Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Dmytro Kuleba, ya ce mayakan sa-kai 20,000 daga kasashen duniya, yawancinsu daga kasashen Turai, za su hada kai da kasarsa domin yi wa Rasha taron dangi.
– Ficewar kamfanonin fasaha –
Netflix ya dakatar da harkokinsa a Rasha, sannan TikTok ya toshe duk sakonnin bidiyo daga can.
– Kafafe yada labarai sun daina aiki –
Kafafen yada labarai na kasashen duniya irinsu BBC, CBC, ARD, ZDF, Bloomberg News, CNN, CBS, RAI da kuma EFE sun daina aiki a Rasha bayan ta yi dokar da ta tanadi hukunci dauri ga masu fitar da rahoton yakin.