Sabbin Masarautun Kano: Kotu ta sanar da ranar shari’a

Babbar kotun jihar Kano ta sanar da ranar 27 ga watan Janairun 2020 don sauraran karar da wasu dattijan jihar suka shigar gabanta, don bukatar dakatar da kirkiro da sabbin Masarautu hudu a jihar Kano. Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya samu rahoton cewa, Alhaji Bashir Usman-Tofa da wasu mutum 19 ne suka shigar da karar […]

Sabbin Masarautun Kano: Kotu ta sanar da ranar shari’a

Babbar kotun jihar Kano ta sanar da ranar 27 ga watan Janairun 2020 don sauraran karar da wasu dattijan jihar suka shigar gabanta, don bukatar dakatar da kirkiro da sabbin Masarautu hudu a jihar Kano.

Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya samu rahoton cewa, Alhaji Bashir Usman-Tofa da wasu mutum 19 ne suka shigar da karar don kalubalantar dokar kirkiro da sabbin masarautun jihar aka yi.

Wadanda ake karar sun hada da: Gwamnan Jihar Kano, Shugaban majalisar Kano, Majalisar dokokin jihar Kano, Atoni Janar na jihar Kano, Tafida Abubakar-Ila, Ibrahim Abdulkadir-Gaya, Dakta Ibrahim Abubakar II, Aminu Ado-Bayero da kuma Majalisar sarakunan Kano.