Sabbin shugabanni: Ga rantsuwa ga azumi
Shekaran jiya Laraba ne sabbin shugabannin kasar nan suka yi rantsuwar kama aiki, inda shugaba Buhari ya yi rantsuwar kama aikin shugabancin kasar nan a karo na biyu. Sai dai kuma a wannan karon shugabannin sun yi rantsuwar kama aikin nasu ne a lokacin da ake azumin watan Ramadan, wata mai dimbin alherai ga al’ummar […]
Shekaran jiya Laraba ne sabbin shugabannin kasar nan suka yi rantsuwar kama aiki, inda shugaba Buhari ya yi rantsuwar kama aikin shugabancin kasar nan a karo na biyu.
Sai dai kuma a wannan karon shugabannin sun yi rantsuwar kama aikin nasu ne a lokacin da ake azumin watan Ramadan, wata mai dimbin alherai ga al’ummar musulmi.
A lokacin da shugabannin suke rantsuwa sun rike Alkur’ani mai girma, mabiya addinin kirista kuma sun rike Baibul, kuma suka yi alkawarin yi wa kasa aiki ba tare nuna bambancin kabila ko addini ko yankin da mutum ya fito ba.
Haka kuma sun yi rantsuwa cewa ba za su taba bin son zuciyarsu a yayin gudanar da ayyukansu ba, sannan kuma za su yi aiki tsakani da Allah ba tare da nuna tsoro ko sabo ba, kuma za su yi wa kowa adalci.
Ana ba shugabanni Alkur’ani ne su rike a yayin da za su yi rantsuwar kama aiki ne saboda su san cewa al’amarin ba na wasa ba ne, Allah zai tambaye su idan suka ci amanar jama’arsu ko suka kasa cika alkawari ko suka yi wa al’ummarsu ha’inci.
To a wannan karon abubuwan karfafawar sun zama guda biyu ga shugabannin da suke musulmi, ga Alkur’ani mai girma ga kuma azumin watan Ramadan a bakinsu a yayin da suka yi rantsuwa. Duk musulmi ya san cewa littafin Alkur’ani ba abun wasa ba ne, saboda haka idan ya rike wannan babban littafin dole ya natsu, domin ba ma za a ba shi ya rike ba sai ya yi alwala, watau sai yana da tsarki.
Bayan haka kuma duk musulmi ya san dimbin darajar da ke tattare da watan Ramadan da alfanun da ake samu saboda yin azumi a cikinsa.
Saboda haka aiki ya samu sabbin shugabanni musulmi da suka yi rantsuwar kama aiki shekaran jiya Laraba, saboda bayan rantsuwa da Alkur’ani mai girma da suka yi tare da alwala, sun kuma yi rantsuwar ne tare da azumi a bakunansu, azumin kuma na watan Ramadana, kuma a cikin goma na karshen watan, watau lokacin da ya fi kowane daraja, saboda a daidai lokacin ne ake samun daren lailatul kadari, daren da ibada a cikinsa ya fi ibadar da da aka yi a wani lokacin da ba shi ba na shekara dubu.
Saboda haka shugabannin sun yi rantsuwar kama aiki da littafi mai daraja a wata mai daraja kuma a lokaci mai daraja, ina fata Allah Ya taimake su su samo wa kansu daraja ta hanyar cika alkawari da rike amana da kamanta gaskiya a yayin gudanar da aikinsu.
Babu shakka rantsuwa babban al’amari ne a wurin dukkan addinan nan biyu, na musulunci da kirista, shi ya sanya ake sanya shugabanni su rantse a yayin kama aiki domin su san cewa Allah zai tambaye su game da wannan nauyin da suka dauka.
Domin haka wadannan shugabannin su ma suna bukatar addu’a ne daga jama’a domin Allah Ya ba su ikon sauke nauyin da suka dora wa kansu. Sai dai kuma a halin yanzu abun ba haka yake ba, saboda gani ake shugabannin sun samu ganima, domin haka ‘yan uwa da abokan arziki kowa sai murna yake yi “namu ya samu,” saboda haka sai murna da annashuwa da shirya liyafa da biyan kudi a kafafen yada labarai ana taya shugabannin murna.
Addu’a da fatan alheri shugabanni suke bukata a halin yanzu, domin ba a san yadda za su kare ba, shin nauyin da suka dauka zai dankare su ne ya kai su gidan yari ko kuma lahira ko kuma za su iya saukewa lafiya? Ba a sani ba.
Ashe kamata ya yi a bari sai sun sauke nauyin da suka dauka an ga sun gama lafiya sannan sai a taya su murna, amma yanzu ba a san yadda za su kare ba, ko shugabancin ya zama masu alheri ya daukaka darajarsu ko kuma ya zama bala’i a gare su, watau ya kai su gidan yari ko gidan wuta a lahira. Shugaban da ya bar mulki lafiya ne yake bukatar a taya shi murna, ba wanda yake kan mulki ba.
Muna fata Allah Ya sa shugabanni su fahimci cewa shugabanci nauyi ne ba ado ba ne, su kuma mabiyansu su fahimci cewa shugabannin abun tausayi ne ba abun sha’awa ba. Domin amana aka ba su ba ganima ba.
Ya kamata talakawa su rage zuwa wuraren shugabanni domin yin maula, kamata ya yi idan suka je wurin shugabanni su je da kokon baransu ne da bukatar a gudanar masu da wadansu ayyuka na cigabansu, ta haka ne za su tamaka wa shugabannin, su kuma taimaki kansu.
Idan har mutane za su rika sanya shugabanninsu a kan hanya idan sun kauce, shugabannin su ma za su rika shiga taitayinsu su rika mayar da hakalinsu wajen yi wa jama’a aiki maimakon mayar da hankali wajen wawure dukiyar jama’ar da suka zabe su.
Allah Ya sa wannan matakin na gaba da ‘yan Najeriya suka shiga ya zama alheri a gare su, Allah Ya tabbatar da alheri, Ya kare dukkan sharri. Allah Ya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.