Sabbin shugabannin ƙungiyar mata ’yan jarida sun kama aiki a Kano

Sabuwar shugabar ta yi alƙawarin yin aiki ba tare da nuna wariya ga mambobin ƙungiyar ba.

Sabbin shugabannin ƙungiyar mata ’yan jarida sun kama aiki a Kano

An yi kira ga mata ’yan jarida da su ci gaba da nuna ƙwazo tare da jajircewa yayin gudanar da aikinsu, wanda hakan zai sa su yi fice tare da kai wa matsayi babban matsayi.

Wannan kira ya fito ne daga Shugabar Mata ’Yan jarida ta Ƙasa (NAWOJ), Hajiya Aisha K. Bura, yayin bikin rantsuwar kama aiki na sabbin shugabannin ƙungiyar reshen Jihar Kano.

Tun da farko a jawabinta na maraba shugabar kwamitin gudanar da zaɓen ƙungiyar, Hajiya Halima Musa, ta bayyana cewa kwamitin nasu ya gudanar da aikinsa ta hanyar bin ƙa’idojin ƙungiyar ba tare da nuna wariya tsakanin mambobinta ba.

A jawabinsa, Shugaban Ƙungiyar ’yan jarida ta ƙasa reshen Jihar Kano, Kwamared Sulaiman Abdullahi Dederi, ya yi kira ga sabbin shugabannin da su yi ƙoƙarin haɗa kan mambobin ƙungiyar ta yadda za a gudu tare su kum tsira tare.

A jawabinta sabuwar shugabar NAWOJ, Kwamared Bahijja Malam Kabara, ta lashi takobin kare haƙƙin mata ’yan jarida musamman waɗanda ake numa musu wariya a wuraren ayyukansu.

Ta kuma yi alƙawarin cewa ƙungiyar za ta riƙa shirya wa mambobinta horarwa a kan sha’anin aikin jarida.

Sabbin shugabannin ƙungiyar mata ’yan jaridar da aka rantsar, sun haɗa da Bahijja Malam Kabara a matsayin Shugaba da Halima Yusuf Angulu a matsayin mataimakiyar shugaba da Maryam Muhammad Yakasai a matsayin sakatariya.

Sauran sun haɗa da Aisha Yalleman a matsayin mataimakiyar sakatariya da Hauwa Salihu a matsayin sakatariyar ƙungiyar da Rabi Bature a matsayin ma’aji da Binta Kabir a matsayin mai binciken kuɗi.

Kazalika, an ƙaddamar da sabon ofishin ƙungiyar da ke harabar Dakatariyar ’Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ).

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo